"Idan na zama 'yar Majalisa Duk Namijin da aka kama yayi Fyaɗe sai an Dandaƙe shi." ---Aisha Balarabe Alaja Katsina ta tsakiya--

"Idan na zama 'yar Majalisa Duk Namijin da aka kama yayi Fyaɗe sai an Dandaƙe shi." ---Aisha Balarabe Alaja Katsina ta tsakiya--


✍️Bishir Umar Zamani Media Crew Katsina


Honorabul A'isha Balarabe Alaja ta bayyana haka wani Shiri na Gangar Siyasa tare da Kafar yaɗa labarai ta Zamani Media Crew, katsina. 

Aisha ta fito Takarar Kujerar Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina, a ƙarƙashin Jam'iyyar APGA mai Alamar zakara, inda a cikin shirin, ta bayyana ƙudiri da guri da take da shi, idan ta samu Nasara a zaɓen da ke zuwa na shekarar 2023. Alaja ta kausasa kwarai akan ko inkula da Gwamnatin APC da ma PDP  suke da shi akan 'yancin mata da Matasa, inda tace "Gwamnatocin da suka gabata basu damu da Al'uma ba, basu damu da 'yancin mata ba, ana yiwa Mata Fyade amma babu wani tsatstsauran hukunci da ake ma wadannan mutanen, ni idan na zama 'Yar majalisa da yardar Allah, duk Namijin da aka kama yayi faɗe ba kisa ba ɗauri, amma dai Dandaƙeshi za'ayi." Inji Aisha

Da take tsokaci a kan abinda yaja har ta shiga jam'iyyar APGA Mai Zakara, Aisha tace "Kai da ganin Zakara Alkhairi ne, kuma jam'iyyar Inyamurai ce, kuma kowa yasan Inyamurai da kwazon nema, don haka manufofin Jam'iyyar mai kyau ne, zamu yi amfani da wannan damar mu samar wa matasa Aikin yi da sana'o'i ga Mata. Zamu tallafawa Mata masu ciki mu taimake su, zamu samar da tsaro saboda kusan shekaru Ashirin da wadannan jam'iyyun suke mulki, basu iya komai ba game da tsaro." 

Aisha Balarabe Alaja dai 'yar cikin garin Katsina ce kamar yanda ta bayyana, wacce tayi karatunta tundaga Matakin Firamare har izuwa jami'a a birnin na Katsina.

Post a Comment

0 Comments