"Idan har Shugaban ƙasa bai tsira daga farmakin 'Yanbindiga ba to babu wani wanda keda Aminci a Najeriya" Farfesa Sani Abubakar Lugga
Farfesa Sani Abubakar Lugga |
✍️Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News
Shehin Malamin Farfesa Sani Abubakar Lugga yayi wannan Zancen ne da Manema Labarai a gidansa dake Katsina bayan gayyatar da Farfesan yayi don yin Buɗa baki, na Azumin Arfa da mafiya yawan Al'ummar musulmi suke yi a ranar ta Arfa domin neman Falala da dace da Al'barkar ranar.
Bayan buɗa baki, da gabatar da Sallar Magriba, Farfesa Lugga yayi ganawar ta musamman da 'Yanjarida inda ya bayyana irin halin da ƙasar Najeriya ta wayi kanta a yau.
Farfesa Sani Abubakar ya bayyana Najeriya akan wani yanayi mafi muni da ta faɗa, inda yace: "Abubuwan da ke faruwa yau a Najeriya, abubuwa ne da suka wuce hankalin Ɗanadam, "Najeriya tana cikin tsaka mai wuya na abubuwa uku, na farko akan halin Tsaro, na biyu akan halin Tattalin arziki, na ukku akan halin Zamantakewa na al'ummar Najeriya."
Farfesa yayi misalai akan haka, inda ya fara da cewa "Koya yasan ankai hari a tawagar Shugaban ƙasar Najeriya, wannan kaɗai ya isa kowa yasan cewa, idan har Shugaban ƙasa bai tsira ba, to waye zai iya tsira a ƙasar nan a yau...? Sarakuna da dama sun ɗage Bikin hawan Sallah, saboda halin tsaro. Wannan ya ƙara tabbatar mana da cewa har su Iyayen Al'umma suna sane da irin halin da ake ciki na tabarɓarewar tsaro."
Lugga ya ƙara bada misali da yanda a kudancin ƙasarnan wasu suka ɓalle suna cewa a basu yankin Biafra, wasu kuma suna cewa a basu Oduduwa, inda wasu daga Arewa (musamman Matasa suna cewa a yanke) inda yace wannan ya isa a gane halin zamantakewa ya lalace.
Farfesa ya bada wani musalai a kan-kansa a shekarar 1980, inda ya saida Buhun Masara a kan Naira shabakwai, su kuma Raguna a wancen lokacin akan naira shabakwai zuwa Naira Talatin ya saida su, yace wannan Ragon da ake saidawa Naira Talatin a wancen lokacin shine yanzu ake saidawa akan kuɗi Naira dubu ɗari hudu.
"Alokacin wanda ya fito daga jami'a ana bashi Naira dubu huɗu da ɗari biyu a shekara, kuma a lokacin Motoci Sabbi ana saida su Naira dubu biyu da ɗari huɗu zuwa dubu uku da ɗari biyar ko da ɗari shida, wannan ya nuna cewa zaka iya bawa ko wane irin ma'aikaci bashin albashin shi, na shekara guda, ya gina gida ko yasai Mota. Lebura ana bashi mafi ƙarancin Al'bashi naira saba'in a wata a yau ance a biya Naira dubu Talatin, kuma a wancen lokaci, Keken hawa Naira biyu ne zuwa Naira huɗu ake saidashi, a she wanda kabawa naira saba'in zai iya saye." Inji Farfesa.
Har wayau Farfesa ya bada misalin a shekarar 1971 lokacin da ya sayi sabon Babur Suzuƙi da Inshora ta shekara ɗaya da Tanki cike, akan kuɗi ƙasa da Naira ɗari huɗu. Inda ya kwatanta halin da ake ciki a yanzu. "A shekarar 1980 na bada Naira ɗari biyar da Hamsin da biyar aka canza mun da Dala dubu a Banki, saboda a lokacin Dalar Amurka guda Daidai take da Sule Hamsin da biyar wato da kaɗan ta wuce rabin Naira, a yau Naira ɗari shida ce daidai." Inji shi.
Yace "Idan aka kalli duk waɗannan sai aga shin mi ya kaimu cikin wannan hali, kuma mu a matsayinmu na Musulmi da Kiristoci, saboda duk ɗan Najeriya miliyan ɗari biyu muna Iƙrarin cewa Mu musulmi ne na kirki Ko mu Kiristoci ne na kirki."
A ƙarshe Farfesa ya ce Allah da kansa a Cikin dukkanin Litattafai Alqur'ani mai tsarki da Bayibul, duka yayi mana dokoki da ƙa'idoji na rayuwa. Don haka yace lallai anyiwa Allah Izgila dayawa, shi'yasa Allah yake azabtar damu.
Inda ya ja hankalin duka ɓangarorin Shuwagabanni da Sarakuna da Malamai. Sannan ya yi kira ga su kansu mabiya (talakawa) da a komawa Allah domin ko Allah ya dubi ga Al'umarsa ya bada mafita, inda yace amma sai kai da kanka ka tashi tsaye ka nunawa Allah kana neman mafita, inda ya kawo ayar Alqur'ani cewa (Innalaha la yugayyuru ma biqaumin hatta yugayyuru ma bi'ankhusihim) da sauran ayoyi da sukayi Nuni da yanda mutum zai nemi Canjin sai Allah ya canza masa.
Zamu kawo maku Cikakkiyar tattaunawa ta hausa da Turanci a shafukan mu, na sada zumunta da tashar mu ta YouTube a Katsina City News TV 📺
0 Comments