Ai ba sai ance jam'iyyar APC ta gaza ba, kowa yasan ta gaza ta ko Ina" -Hon Abubakar Rabi'u Dutsinma Dan takarar Majallisar Jaha karkashin Jam'iyyar NNPP-

"Ai ba sai ance jam'iyyar APC ta gaza ba, kowa yasan ta gaza ta ko Ina" 

-Hon Abubakar Rabi'u Dutsinma Dan takarar Majallisar Jaha karkashin Jam'iyyar NNPP-

Ahmad Badamasi Zamani Media Crew ✍

Kamfanin Zamani Media Crew yasamu  bakuncin Dan takarar  majallisar Jiha a karkashin inuwar Jam'iyyar NNPP Hon Abubakar Rabi'u Dutsinma a Cikin Shirin Gangar Siyasa.

Dantakarar yace " duk da a baya muna jam'iyyar APC daga bisani muka yanke shawarar Dawowa jam'iyyar NNPP saboda itama jam'iyyar PDP ta Gaza a lokacinta, Saboda hakane na koma jamiyyar NNPP har nake takara a cikinta."

Idan Allah yabani nasarar zama Dan majallisa zanbude ofis a cikin karamar hukuma Dutsinma Danjin koken Al'umma, kuma ko ina bazan jeba inanan a cikin Dutsinma saboda nan ne tushen mu inji Hon Abubkar.

Dantarar yakara da cewa matsalar tsaro kuma ba haki bane na karamar hukuma ko jaha aa haki ne na gwamnatin taraya saboda su sukeda sodoji, yansanda, Civil Defence da sauransu to shima zamuyi bakin kokarinmu wajen ganin mun fadakar da wanda ke da alhaki da  abun.

Dan majallisa taraya mai wakiltar karamar hukumar kurfi/Dutsinma Hon Armaya'u Abdulkadir yayima Al'umma yankinshi ayukan duk wasu alkawura da gwamna Aminu Bello Masari baiyiba dukda bashi yayi Alkawarin ba kuma muna alfari dashi a cikin jam'iyyar mu ta NNPP.

Daga karshe dan takarar yayi ikirarin cewa mutanen garin dutsinma wayayu ne sun san kansu, ba Jam'iyya suke yiba mutum suke yi, ko a wace jam'iyya mutum yafito idan yana da Nagarta zasu zabeshi.

Post a Comment

0 Comments