Daga Auwal Isah.
Masarautar Kasar Katsina a ranar Asabar din nan 11 ga Yuni 2022, ta yi taron nadin Sanata Ibrahim Ida a matsayin sabon Wazirinta.
Nadin Wazirin wanda Sarkin na Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya yi, ya gudana ne a farfajiyar fadar Masarautar, taron nadin da ya samu halartar dimbin al'umma daga sassa daban-daban daga masarautun Nijeriya da na ketare.
An dai nada Sabon Wazirin ne bisa cantarshi ga Sarautar biyo bayan shiga jerin masu neman karagar Sarautar Wazirancin da ya yi, bayan da tsohon Wazirin Masarautar, Alhaji Sani Abubakar Lugga ya yi murabus daga Wazirancin Masarautar a ranar 24 ga Fabrairun 2022.
Nadin sarautar ya samu halartar manya-manyan mutane da suka hada Attajirai, Sarakuna, Jami'an Gwamnati da 'yan jarida.
Daga cikin wadanda suka halarci nadin akwai Sarkin Kano mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayaro wanda ya samu wakilcin Kadi Muhamad Inuwa Aminu, da Marafan Dawakin Zazzau Alhaji Shehu turaki, Dan-goriban Zazzau Alhaji Aminu Zaki da sauransu.
Da yake jawabi jim kadan bayan ya yi nadin, Sarkin kasar Katsina mai martaba Alhaji Abdulmuini Kabir Usman ya bada shaida dangane da kyawawan halayen sabon wazirin da irin taimakonsa ga al'umma.
Shi ma a nasa jawabin, Sabon Wazirin, Sanata Ida, ya sha alwashin ci gaba da ayyukan alkhairi tukuru ga Masarautar da talakawa wadanda ya taho da su tun tale-tale.
Kafin nadin nasa, Alhaji Ibrahim Ida shi ne mai rike da sardaunan Katsina.
An dai haifi Ibrahim Ida a a cikin birnin Katsina a shekarar 1949, inda ya yi karatunsa a cikin kasa Nijeriya, Birtaniya da kuma Amurka.
Haka nan kuma ya rike manyan mukamai a aikin gwamnati da ya yi, inda ya rike mukamin babban sakataren ma'aikatar tsaron Nijeriya, ya kuma yi aiki da babban bankin Nijeriya da sauransu.
A mukaman Siyasa da ya rike kuwa, ya wakilci shiyyar Katsina ta tsakiya a majalissar dattawar Nijeriya tsakanin 2007 zuwa 2011.
0 Comments