Gwamnatin Zamfara ta bai wa 'yan jihar damar mallakar bindiga


Gwamnatin Zamfara ta bai wa dukkan 'yan Jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

A wata sanarwa da Kwamishinan watsa labaran Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya aike wa manema labarai ranar Asabar, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren 'yan ta'adda da 'yan fashin daji kamar yadda BBC ta ruwaito. 

Gwamnatin Zamfara ta dauki matakin ne watanni da dama bayan gwamnatin Jihar Katsina da ke makwabtaka ta umarci mazauna jhar su mallaki bindiga domin kare kansu daga masu kai hare-hare.

"Hare-haren ta'addanci sun kasance abin damuwa ga jama'a da gwamnatin jiha. Don haka ne, domin mu magance wannan matsala baki daya a yankunanmu, gwamnati ba ta da zabin da ya wuce daukar matakan da suka hada da bai wa mutane damar shiryawa da kuma mallakar bindigogi domin kare kansu daga 'yan fashin daji," in ji sanarwar. 

Ta kara da cewa gwamnati ta umarci Kwamishinan 'yan sanda ya bai wa dukkan mutanen da suka dace da kuma suke bukatar mallakar bindiga su mallake ta domin kare kansu.

Gwamnatin ta Jihar Zamfara ta ce ita da kanta za ta shige gaba wajen ganin an saukaka wa mutane hanyar mallakar bindiga, musamman ga "manoma domin samun makaman da za su kare kansu."

"Tuni gwamnati ta kammala shirin raba fom 500 ga masarautu 19 da ke Jihar nan domin bai wa mutanen da ke bukatar mallakar bindigogi domin su kare kansu," a cewar sanarwar.

Jihar Zamfara na cikin jihohin da suke fama da matsananciyar matsalar tsaro a Najeriya sakamakon hare-haren 'yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

Wadannan hare-hare sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da raba dubbai daga muhallansu.Katsina City News

Gwamnatin Jihar da kuma ta tarayya sun sha yin alwashin kawo karshen wadannan hare-hare, sai dai matsalar ta ki ci ta ki cinyewa.

Post a Comment

0 Comments