Dirar masu garkuwa da Mutane a Shola da Checeniya, wane hali Mutanen Unguwar suke ciki...?

Dirar masu garkuwa da Mutane a Shola da Checeniya, wane hali Mutanen Unguwar suke ciki...?

Zamani media crew Katsina

A daren ranar Litinin wayuwar garin Talata na satin da ya gabata ne, wasu masu garkuwa da Mutane suka Dira a wata Unguwa da ake kira Shola Quaters, da wani yankin Unguwar Checeniya duka a bayan Babbar Asibitin koyarwa ta Gwamnatin Tarayya, dake cikin garin Katsina inda suka kwashi mutane suka gudu dasu.

 

Rahotanninn sun ce, ƴan bindigar sun shiga unguwar ne ɗauke da bindigogi a saman Babura, inda suka ɗauki wasu Mutane suka ranƙaya Daji da su.

 ko da yake ba su kashe kowa ba, amma sun tafi da maza shidda da matar aure É—aya da kuma É—iyarta Æ´ar shekara biyu da haihuwa. Ya zuwa haÉ—a wannan rahoton sun saki mutum guda.

Tun bayan faruwar lamarin mazauna Unguwar ta Shola suke zaman zullumi a bisa baraza da suka ce ana yi masu daga É“angaren masu garkuwa da Mutanen. Mun nemi jin tabakin wasu mazauna Unguwar a cikin tsoro da shakku sun shedamana cewa "tun bayan faruwar lamarin, 'yanjarida sun shigo sunyi fira da wasu mazauna Unguwar, amma daga bisani sai suka dunga bugo waya suna cewa sunji wane yace kaza- wane yace kaza, sana kuma a gefen jami'an tsaro kuma sun sheda masu cewa su daina fira da 'yan jarida saboda suna É“ata masu aiki.

Kamar yanda wani da yaso a sakaya sunansa kuma abin ya ritsa da shi, ya sheda mana cewa, "Yanzu haka kunga halin da nake ciki, amma duk da haka bamuyi ƙasa a guiwa ba, muka sanar da jami'an tsaro alokacin da abin ya faru, munje CPS domin neman dauki amma 'yansanda uku kaɗai muka iske suna Bacci sai da muka tadasu, a karshe sai suka cemana, ai Matsalar yanzu masu garkuwa tuni sun riga sun kama gabansu ko sunje ba wanda zasu gani, mu bari sai da safe sai mu dawo muyi Report." Inji wani mazaunin Unguwar.

Wani kuma du a cikin mazauna Unguwar, ya shedawa Katsina City News, cewa sunji wani jami'in ɗansanda yana cewa wai ai Unguwar bama cikin Katsina take ba, kuma munzo munyi gidaje babu tsari, mun fasa Katangar Gwamnati muna bi ta ciki, yace inda kuke gani na nan zaune gonar mahaifi na ce gadon wajen nayi, kuma dukkanin mu, mafiya yawa gonakin mu ne, muka gina muke zaune, idan ba Katsina muke ba to sai a faɗi mana wane gari muke...? Kuma ko ba Katsina muke ba ai mutane ne, muna da Haƙƙin tsare dukiya da rayuwar mu. Injishi.

Lamarin Garkuwa da mutane ya ta'azzara ba a wasu yankuna na Jihar Katsina ba, kusan da jihohi shida daga arewacin Najeriya, inda da wahala a kwashe sati ba tare da an tare ko an an dira gidan wasu ba, duk da kokarin da hukumar 'yansanda ta jihar Katsina a kusan kullum mafiya yawan lokuta sai sun bayyana irin nasarorin da suke samu na É—akile waÉ—annan É“ata gari ga Manema Labarai.

 

Post a Comment

0 Comments