Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafar nan Sadio Mane ya yi abin a zo a gani a mahaifarsa ta ƙauyen Bambali da ke ƙasar Senegal.
Wannan bawan Allah, Mutanen Ƙauyenshi suna alfahari da shi sakamakon irin ayyukan ci gaba na alheri da ya samarwa jama'ar kauyen nasu.
Waɗannan su ne irin ayyukan da Ɗan wasan ƙwallon ya shuka a mahaifar tasa ta Bambali, wadanda suka hada da:
1. Ya Gina makaranta da darajarta ta kai Kudi €270,000.
2. Ya Gina Asibiti a kan Kudi €530,000.
3. Yana ba wa kowanne Iyali Kudi €70 duk wata a Æ™auyen nasu.
4. Yana bayar da tufafi kyauta ga ƙananan Yara.
5. Ya Samar da hanyar sadarwa mai ƙarfin 4G a ƙauyen nasu haɗin gwiwa da Kamfanin Orange.
6. Ya Gina gidan mai na Oryx Senegal duk dai a cikin ƙauyen nasu.
Sannan kuma ya ce zai samar da filin wasan ƙwallon ƙafa a ƙauyensu na Bambaly cikin watanni 5 zuwa 6.
A cikin wani jawabinsa, ya ce "duk abin da na samu na Senegal ne, kuma tabbas wannan abin zai kasance a cikin Bambali." In ji shi.
Anya a kaf faɗin ƙasashen Afirka an ta6a samun ɗan wasa kamar Sadio Mane kuwa?
0 Comments