ZAƁEN 2023: Matasa Sunyi Kira Ga Shugaba Buhari Da Ya Marawa Osinbajo Baya

ZAƁEN 2023: Matasa Sunyi Kira Ga Shugaba Buhari Da Ya Marawa Osinbajo Baya

DAGA Alaramma Ibrahim Gwale

Matasa da dama a fadin kasarnan sunyi Kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya marawa Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo baya a takarar da yakeyi ta Shugabancin Kasarnan na shekarar 2023. 

Matasan sunyi wannan kirane  a shafuka da dama na yanar gizo,  wanda hakan yaja hankalin sauran matasa da dama. Daganan ne kuma abin ya bazu, inda dubban mutane suka shiga sahun matasan wajen Kira ga Shugaba Buhari akan ya saurari kokensu.

Daya saga cikinsu yace kasancewar Farfesa Osinbajo yayi aiki da Buhari, don haka yafi kowa can canta  kuma Shugaba Buhari yagamsu da gogewa da jajircewa da yake da ita.

"Wani mutum yake cewa, Shugaba Muhammadu Buhari shine babban DELIGET a zaben fidda Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar APC. Hakika na yarda da wannan magana. Duk wanda ya nuna, tabbas shine zaiyi nasara. 

"Na tabbata Baba Buhari zai marawa Mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo baya. Sunyi aiki atare, kuma yasan irin gogewa da yake da ita da kuma irin jajircewa ta siyasa da mulki. Baba Buhari muna rokonka, Dan Allah ka tsayar mana da Osinbajo a matsayin Dan Takararmu,"

Post a Comment

0 Comments