Fitacciyar jaruma kuma furodusa a masana’antar Kannywood, Hajiya Hannatu Bashir (wadda aka fi sani da Hanan), ta ƙalubalanci mawaƙi a Kannywood, Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) da ma duk wasu mutane ire-irensa da su ke sukar ‘yan fim a kan rashin kamun kai ko rashin asali, inda tw bayyana cewar mafi yawan masu yin wannan maganar wasu ‘yan fim ɗin ma sun fi su asali.
Jarumar ta kuma bayyana dalilinta na rashin damuwa da sukar da ake yi masu, a cikin tattaunawar musamman da ta yi mujallar Fim a kwananin nan a Kano. Ga yadda hirar ta kasance:
FIM: Hannatu Bashir, kina ɗaya daga cikin jarumai mata a masana’antar Kannywood, to kuma an daɗe ana sukar mata game da abubuwan da su ke gudanarwa, wanda ba ma na waje ba har abokan sana’ar ku su na yi maku wani kallo. Ko me ki ke ganin ya jawo hakan?
HANAN: To, a gaskiya abin da zan ce yana kawo waɗannan abubuwan zan iya cewa wasu abubuwan mu na faɗa ne kawai don so zuciyar mu. Idan ka ɗauko maganar ‘yan waje, wani abu ne a cikin zuciyar su, tun a da ba tun yanzu ba. Abin da ya ke faruwa, su na kallon mata ‘yan fim ba wani abu ba, kawai su na kallon matan fim ‘yan iska; in ka tambaye su dalili, ba su da shi. Abin da ya sa kullum nake kallon ba su da dalili, idan su ka ce sana’ar fim ana yin shi maza da mata, kowace sana’a maza da mata ake yin shi. Me ya sa ba a kallon wannan sana’ar a lalatacciyar sana’a ko kuma a gurɓatacciyar sana’a sai sana’ar fim? Sannan kuma in ka duba, na biyu, yadda kowa ke fita ya yi sana’ar sa, haka mu ma mu ke fita mu yi sana’ar mu. Idan kana tunanin shago ne da kai, idan ka fito ka kasa kaya mutane dubu su na wucewa, haka mu ma haka idan mun dasa kyamara za mu ɗauki fim, mutane dubu su na kallon mu. To kusan wani abu ne da muke yin shi a buɗe, ba ɓoyayyen abu ba ne. Kar ka ce ka ga mace a a falo ita kaɗai ce, daga ita sai namiji a falo, mutane dubu ɗari ne a bayan kyamara: wala’alla akwai mai kyamara, akwao mai ‘spund’, akwai mai ‘costume’, akwai mai ‘makeup’, mutane da yawa su su ke bayan kyamarar, idan an zo editin ne ake yankewa a nuna iya wa’inda ake so a gani. To kullum ‘yan kallo da mutanen gari sun kasa fahimtar wannan, su ke kallon matan fim a ‘yan iska. Yau idan macen fim ta yi aure kullum abin da za a fara cewa, “Allah ya sa ta zauna; ai ba za ta zauna ba!” In ka tambayi yawancin ‘yan wajen Kannywood dalilin su na zagin ‘yan fim, ba su da shi. To, ɗan fim ya zama kamar madubi ne a duniya. Idan ka na da madubi a ɗakin ka, kullum ka tashi da safe madubin za ka fara kalla. To ko yaya ya ɗan ɓantare ya tsage, za ka gane ya na da matsala saboda da man shi ka sa a gaba. To haka mu ke a cikin mutane, kullum ana bibiyar ana tunanin me mu ke yi. Kafin auren ‘yar fim ɗaya ya mutu sai aure dubu ya mutu a cikin gari, amma ba za a ce ba saboda ba a san su ba, ba a bibiyar su. Amma naki ‘yar fim, ko ya ya mutu, zai zama abin magana.
FIM: Ana ganin ku na yin abin ku ne a buɗe, maimakon wasu abubuwan ku riƙa yin sa a sirri.
HANAN: E to, kusan ɗan fim da wahala ka ce ya na yin wasu abubuwan sa a buɗe, saboda daga lokacin da ka zama ɗan fim abubuwa da yawa a rayuwar ka ma kasa yin su ka ke yi saboda gudun kar za zage ka. Yau kunya ma ka ke ji ka fito titi. Za ka sa niƙab za ka sa ‘face mask’, za ka yi waye, za ka kare fuskar ka. Wani abin in ka ga an yi shi, to sai abin da ya zama dole. Saboda ba zai yiwu in shiga guri ka ce min me ya sa na shiga ba, ba zai yiwu na wuce a layi a ce ga ta can ba. To kuma saboda ina gudun a ce ka ga can ɗin ya zama ko yaushe ina musguna wa rayuwa ta ba, gaskiya ba zai yiwu ba! Wannan ya saka wani abin za ka ga ake zagin mu da shi ko kuma ake jifar mu da shi. Wani abin ne ba yadda za mu yi, dole ne za mu fito mu yi rayuwar mu kamar yadda kowa ya ke yi. Amma rayuwar mu mu fito mu yi kamar yadda kowa ya ke yi ya zamar mana tashin hankali saboda ko ya mu ka yi, tuntuɓen abin da mu ka yi ake nema, ba alkhairin mu ba. Sai mu yi alkhairi dubu ba a yaba mana ba, amma lpkacin da mu ka yi kuskure ɗaya sai a hau mu da zagi, a hau mu da baƙaƙen maganganu. Waɗanda su ke iyayen mu ma, waɗanda za su iya kiran mu su ba mu shawara, su ja hankalin mu, to da su za a haɗu da yaran duk a ci gaba da zagin mu da ci mana mutunci.
FIM: To baya ga su ‘yan wajen harkar, a cikin ‘yan fim ma ana kawo irin waɗannan maganganu da sukar, musamman idan ki ka auna irin maganganun da Naziru Sarkin Waƙa ya yi kwanakin baya.
HANAN: To, idan ka ɗauko maganar ‘yan ciki, su kuma wannan su na yin shi ne don son zuciyar su. Sannan kuma abin da na ke so kullum na riƙa gaya wa ‘yan ciki shi ne sana’ar fim dai sana’ar ka ce, in ka zagi fim kan ka ka zaga, idan sunan ka ɗan fim sunan ka ɗan fim, sunan yaran ka ‘ya’yan ‘yan fim, ba ka isa ka canza wannan sunan a matsayin ɗan fim ba, ba ka isa ka canza sunan ‘ya’yan ka a matsayin yaran ɗan fim ba. To, idan ka ɗauko maganar Naziru, kullum ina faɗa, idan ba zai faɗi alkhairin Kannywwod ba kamata ya yi yai shiru. Kusan abubuwa da yawa da ya ke faɗa ba haka ba ne. Ya na janyo hankalin mutane su ci gaba da zagin Kannywood, ya na ɓata darajar sana’ar da mutuncin ta. Amma ya kasa ganewa sunan shi mawaƙi, sunan yaran shi yaran mawaƙi, ko ya mutu gobe sunan ‘ya’yan shi yaran mawaƙi. Idan ya na tunanin yanzu a matsayi na na mace, idan ya yi wani surutun ‘yan gari za su zage ni, wasu ma za su yi tunanin yadda ya ke magana a kan matan ‘yan fim ya za a yi mu aure su, ya na da yara mata. Sunan yaran sa dai yaran mawaƙi. Idan ya na tunanin ya ɓata alaƙar rayuwar wata mace a fim, to ya taɓa har da ‘ya’yan sa. To duk idan mu na tunanin irin wannan abubuwa, to akwai abubuwa da yawa wanda za mu kare, ba za mu dinga yin su ba. Abubuwa da yawa da Naziru yake faɗa ba gaskiya ba ne!
FIM: Ba kya ganin cewa shi ɗan ciki ne, ya san duk wasu abubuwa da su ke faruwa?
HANAN: A’a, shi ma da bakin sa ya faɗa cewa shi ba ɗan fim ba ne. Ka ga kenan bai ma kamata ya faɗi abin da ya shafi ciki ba. Kamata ya yi ya faɗi abin da ya shafi waje tunda ya ce shi ba ɗan fim ba ne. To tunda ya barranta kan shi da ‘yan fim to bai kamata ya riƙa fitowa ya na bada labarin ‘yan fim ba. Kuma abin da na ke so a gane shi ne da fim da waƙa abu ɗaya ne, masana’anta ɗaya ake, tare ake, to ba ka isa ka ce ka na mawaƙi ka cire kan ka daga fim ba, sunan ka dai ɗan fim, tunda dai masana’anta ɗaya ce kuma abu guda ake yi. Ɗan fim me ya ke yi ne? Bidiyo ya ke fitowa ya yi a duniya a gan shi; haka mawaƙin ma idan ya yi odiyo ya na fitowa ya yi bidiyo an gan shi a duniya. To duk wani abu ne daban. Kullum sai mu na nesanta tunanin mu, mu na faɗar alkhairi ne a junan mu, za mu samu zaman lafiya. Albarka mu ke nema a masana’antar gaba ɗaya. Sannan fatan mu shi ne haɗin kan mu da zaman lafiyar mu shi ne zai bada abin da ake so. Su kuma ‘yan gari, duk lokacin da ya fito ya yi surutu su na jin daɗi su na goyon bayan sa, to da ma abin da su ke jira kenan, kullum abin da su ke ‘expecting’ kenan su ji an ce a kan ɗan fim, to kuma ga wani a ciki ya fito ya faɗa, me zai hana ba za su yarda ba? Wani abu ne wanda su ka daɗe su na sukar mu da shi, sama da shekaru wanda mu mun sani amma ba ma damuwa. Ni kullum abin da ya sa bai yaɓa damu na ba, duk zagin da ake wa ɗan fim, abu ɗaya ne zuwa biyu. Na san makullin Wuta da Aljanna ba a hannun kowa ya ke ba. To tunda na tabbatar da cewa makullin Wuta da Aljanna ba a hannun kowa ya ke ba, to duk yadda ka zage ni ba zan damu ba, saboda na san me na ke yi. Wani da ya ke zagin ‘yan fim, wasu da yawa mun fi su asali da tarbiyya, mun fi su ilimi, mun fi su komai, amma za su fito su zage mu. Ba za mu damu ba saboda Allah ya san me mu ke yi. Kowa da irin rayuwar sa. Idan mun yi daidai Allah ya sani, in ma mun yi ba daidai ba Allah ya sani. To, tunda hukuncin ba a hannun kowa ya ke ba, to sai mu bar su Allah ya kai mu lokacin da komai zai bayyana.
FIM: A matsayin ki na ‘yar fim, wanne irin kallo ko mu’amala ki ke so mutane su yi maku?
HANAN: E, a matsayi na na ‘yar fim kallon da na ke so da kuma mu’amalar da na ke so mutane su yi mana su rinƙa kyautata mana zato. A duk lokacin da su ka kyautata mana zato, to mu ma in-sha Allah za mu ji daɗi saboda kusan abin da su ke yi mana a cikin ɗari kashi 80 zargi ne. To shi menene hukuncin zargin a addinance ma idan ka ɗauko shi? Wani abu ne kusan wanda bai ma kamata mu dinga yi wa junan mu ba. Saboda wata ƙasa ce da mu ke ciki ta al’adar mu. “Da fim da waƙa abu ɗaya ne." To akwai irin abubuwan da ya kamata mu ma mu riƙa kiyayewa. Mu daina yi wa junan mu mummunar fahimta, mu daina yi wa junan mu mummunan zato. Su dinga yi mana kyakkyawan zato, su ɗauka cewa su na da yara, wasu su na da ƙanne. Su ɗauka mu ‘ya’yan su ne, su ɗauka mu ƙannen su ne, su ɗauka mu iyayen su ne; idan ‘yar’uwar ka ce ko yayar ka ce a ciki, a matsayi na ka ɗauke ni na zama ƙanwar ka ko yayar ka, idan na fito a masana’antar fim za ka zage ni ne? Wala’alla ba za ka zage ni ba saboda ni taka ce, to ka ɗauka ni ɗin ‘yar’uwar ka ce, ba sai ka zage ni ba. Wala’alla idan wani kuskure ka ga na yi a matsayi na na ‘yar fim, za ka iya gyara min ba tare da ka zage ni ba, ba tare da ka ce mini ‘yar Wuta ba, “duk wani ɗan fim ɗan Wuta ne.” To menene hukuncin ka da ka ce duk wani ɗan fim ɗan Wuta ne? Ka san ɗan Wuta ka san ɗan Aljanna? Ba wanda ya san ɗan wuta babu wanda ya san ɗan Aljanna. Kyawawan ayyukan ka su za su kai ka Aljanna, munanan ayyukan ka su za su kai ka Wuta. To ya danganta da kyawawan ayyukan ka, ko ba ka yi fim ba, munanan ayyukan ka da ka ke a duniya su ne za su kai ka Wuta; wala’alla ni da na yi fim na yi kyawawan ayyukan da za su kai ni Aljanna. To wannan abin ya kamata mu riƙa tunani wa junan mu, mu ƙaunaci junan mu, mu zauna lafiya.
FIM: To madalla. Mun gode.
HANAN: Ni ma na gode.
0 Comments