Yakin Neman Za6en Abbas Umar Masanawa Ya Sa Jihar Katsina Cika Da Batsewa.


Daga Auwal Isah.

A ranar Talata 17 ga Mayun 2022, dan takarar gwamnan jihar katsina a karkashin jam'iyyar APC, Abbas Umar Masanawa, wanda inkiya da Makararre (Letcomer) ya fito yakin neman za6ensa, za6en da ke zuwa suar kwanaki uku kacal a matakin fidda gwani (primary election)

Dan takarar wanda a iya cewa ya fito takarar daga baya, wanda kusan sai da kowane dan takarar a jam'iyyar ya gama sayen fom dinsa, ya girgiza daukacin birnin na Katsina a yayin gudanar da yakin neman za6en nasa.
Masanawa dai ya yanki Tikitin Takararsa a bababn birnin tarayya Abuja ne, ana saura kwanaki goma za6en fid da gwani.

Abbas Masanawa, ya shigo jiharsa ta katsina a ranar Litinin bayan da uwar Jam'iyyar APC ta tantance shi a Abuja inda jam'iyyar ta bayyana cancancartarshi na shiga a fagen daga a fafata da shi a cikin rukunin mutane tara wadanda za su fafata a za6en fid da gwani da za a gabatar a ranar 20 ga Mayu, 2022.
A yayin da Zamani Media Crew ke daukar rahoton yakin neman za6en takarar, ta shaidi yadda dimbin magoya bayansa suka fito suka yi farin dango a fadin jihar, inda suka tarbe shi, sa'annan aka rankaya da shi zuwa Ofishin jam'iyyar ta APC, inda a can ya gabatar da kansa tare da tabbatar wa shuwagabannin Jam'iyya cewa shi ma ya zz cike da bukatuwar a fafata da shi a za6en fid da gwani bayan ya cika dukkakn sharuddan kundin za6e da na jam'iyyar.
A cikin jawabin da ya gabatar, Abbas ya kuma tabbatar wa shuwagabanni cewa shi mai matukar biyayya ne, kuma muddin Allah ya ba shi sa'ar darewa wannan kujera, zai tafi kafada da kafada da kowa da kuma bin ka'idojin jam'iyya. 

A yayin tarbar, daukacin shugabannin jam'iyyar na jiha ne suka tarbe shi wadanda suka hada da;  Shugaban Jam'iyyar, Mataimakin shugaban, Sakatare, da sauran al'umma ciki har da Shugaban jam'iyya na Æ™aramar hukumar na jihar ta Katsina.
Su ma a nasu 6angaren, shugabannin jam'iyyar na Katsina sun yaba kan kwazo da kirkin dan takarar, kuma sun tabbatar masa da yin adalci a wajen gudanar da za6en da za a gudanar.

Biyo bayan kammala wannan, dan yakarar ya shiga cikin kwaryar birnin Katsina shi da dubban magoya bayansa, inda ya zagaya tare da gaisawa dimbin jama'a, gaisawar da ta kai shi har zuwa kimanin karfe 9:00 na dare, inda daga nan ya wuce Taron manema labarai a dakin taro na MUNAJ EVEN CENTER da ke kan Titin gidajen Fatima Shema.
Ya yin ganawarsa da manema labarai, dan takara ya bayyana wa Al'ummar jihar Katsina (ta hannun manema labarai) Ƙudurorinsa dalla-dalla, inda a ciki ya zayyano matsalolin da jihar Katsina ke fama da su, ya kuma yi bayanin yadda zai bi wajen kawo karshensu.

Har wayau, dan takarar ya tabbatar da cewa zai bi turbar da Mai gidansa Gwamna Aminu Bello Masari ya bi wajen ciyar da Katsina gaba, inda ya bayyana cewa duk dan jihar Katsina zai yi tinƙaho da Gwamnatinsa muddin Allah ya ba shi nasara.

Masanawa ya kuma bayyana cewa, idan kuma Allah bai ba shi nasara ba, to a shirye yake wajen dafawa don kawo ci gaba ta hanyar aiki ga duk wanda Allah ya ba nasarar, inda ya ce "...saboda ba mu da kamar jihar Katsina."

Daga karshe, arshe Abbas Masanawa kar6a tambayoyi daga manema labarai, inda ya rika amsa su daki-daki.
Dan Jarida: "Me ya ta6a yi wa al'ummar jihar Katsina da za ka fito takara da rana tsaka bayan ga wdanda aka sani kuma sun yi wa al'umma abin a zo a gani?"

Abbas Masanawa: "Shekaru ashirin da suka gabata, na kafa wata cibiya ta biya wa dan Katsina tallafin karatu kuma har yanzu cibiyar na aikinta yadda ya kamata, da sauran ayyukan raya kasa irin su Bohol-Bohol, Masallatai da sauran su"

Abbas Umar Masanawa dai kafin ya aje aikinsa ya fito takarar gwamnan jihar ta Katsina, shi ne tsohon babban daraktan Ma'aikatar buga KuÉ—i da wasu muhimman takardun Gwamnatin tarayya.

'Yan magana dai na cewa; "ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare. Sannan, Allah ya ba mai rabo sa'a."

Post a Comment

0 Comments