Daga Auwal Isah.
Dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar PRP, Alhaji Imran Jino, ya bayyana tare da bada tabbacin cewa shi ne zai ci za6en shekarar 2023 a matsayin gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyarsa ta PRP.
Dan takarar ya bayyana haka ne a lokacin da yake shelanta fitowarsa takarar kujerar gwamnan jiha a jam'iyyar PRP a dakin taro na 'Service Of Humanity' a ranar Lahadin nan.
A yayin da yake gabatar da kudurorinsa a matsayinsa na dan takarar gwamnan, ya tsawaita bayani tare da muhimmantar da abubuwa kamar haka da zarar ya kai ga kujerar. Abubuwa da suka hada da; Samar da Tsaro, Inganta wutar Lantarki, Inganta Noma, Inganta Sanan'o'i ta hanyar bayar da tallafi musamman ga Mata da suke iyayen al'umma da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.
"In Allah ya yarda za mu yi taron biki na nasarar lashe za6en gwamna a watan Mayu 2023." In ji shi.
"A karkashin jam'iyyar PRP za a rantsar da gwamnan jihar Katsina." Ya sha alwashi.
Taron shelanta takarar tasa dai, ya samu halartar dimbin al'umma da suka hada da masu ruwa da tsaki a matakin kananan hukumomi, jiha da kuma kasa baki daya.
Taron ya kuma samu halartar wakilin jam'iyyar PRP na kasa Alhaji Halliru Umar, Uban jam'iyya a matakin jiha Alhaji Abdurrahman Abdullah MNI, shugaban jam'iyyar na jiha Alhaji Hamisu Hassan Kankara, shugaban masu tantance 'yan takarar jam'iyya Dr. Halliru Mamman, dan takarar Majalissar wakilai na tarayya na jiha a karkashin jam'iyyar Usman Buhari da saurarnsu.
Sauran sun hada da dimbin masu za6en shugabanni(delegates), sai magoya baya maza da Mata, Matasa, Dattijai da sauransu.
Bayan kammala shelanta takarar tasa, Alhaji Imran Jino ya kuma ja tawagar magoya bayansa inda ya kewaya a cikin birnin na katsina domin kara shelantawa da sanar da sauran jama'a ayyana takarar tasa a karkashin jam'iyyar ta PRP, zagayen da ya samu rakiyar jami'an tsaro da 'yan jarida.
0 Comments