Kiristocin 'Yan Nijeriya Fiye Da 10,000 Za Su je Bauta Isra'ila Da Jordan.


Ana sa ran akalla kiristocin Nijeriya 10,000 ne a bana za su tafi ziyarar bauta a kasashen Isra'ila da Jordan.
Pam ya ce bana an hada da Jordan a cikin wuraren da matafiya za su ziyarta bautar baya ga isra'ila, saboda a wurin ne Yahaya mai baftisma ya yi wa Yesu Almasihu baftisma, hakazlika kuma a wannan wurin ne Annabi Musa ya yi wafati.

Sannan kuma Pam ya kara da cewa, daga Jordan din dai ne aka dauki Annabi Elijah zuwa sama.

Post a Comment

0 Comments