Alhaji Umar Abdullahi Tata ya ziyarci hedikwatar jam'iyyar APC ta jihar Katsina domin ya kaddamar da takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Katsina a zaben 2023 dake tafe.

Alhaji Umar Abdullahi Tata ya ziyarci hedikwatar jam'iyyar APC ta jihar Katsina domin ya kaddamar da takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Katsina a zaben 2023 dake tafe.

Tata ya ziyarci hedikwatar jam'iyyar ne tare da dumbin magoya bayan sa daga dukkan sassan jihar Katsina a ranar Laraba.

Umar Tata dai ya yi takarar Gwamnan jihar ta Katsina a zaben 2015 a jam'iyyar APGA ya kuma nemi tikitin takarar a jam'iyyar PDP a zaben 2019.

Da yake jawabi a hedikwatar jam'iyyar gaban Shugabannin jam’iyyar na jiha, Tata ya ce idan Allah ya ba shi nasara zai mayar da hankali ne wurin samar da tsaro are jihar ta yadda cikin shekara daya ba za'a sake kashe mutum a jihar ba.

Haka zalika Tata ya sha alwashin idan Allah ya ba shi nasara zai sake gina garuruwan da 'yan bindiga suka tada tare da mayar da kowa gidan shi ya kuma ba su jari domin su cigaba da rayuwar su kamar da.

Mataimakin shugaban jam'iyyar, Alhaji Bala Abu Musawa wanda ya tarbi dan takarar a madadin sauran Shugabannin jam’iyyar ya yaba masa tare da yi masa addu'ar samun nasara.

Bala Abu ya kuma tara da tabbatar masa da cewa jam'iyyar za ta yi ma kowa adalci a zaben cikin gida na fitar da gwani da za'a yi.

Daga bisani, Alhaji Umar Abdullahi Tata ya jagoranci dumbin magoya bayan na shi zuwa filin Kangiwa dake gaban fadar mai Martaba Sarkin Katsina inda ya yi jawabai ga magoya bayan sa. Majiya: Zamani Media Crew.

Post a Comment

0 Comments