YANZU-YANZU: APC ta ƙaiyade N100m a matsayin farashin form ɗin takarar shugaban ƙasa
Masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC, za su biya naira miliyan 100 domin mallakar fom kafin su shiga zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a watan Mayu.
Sakataren Yaɗa Labaran APC na ƙasa, Felix Morka ne ya sanar da hakan jim kaɗan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar na ƙasa karo na 11 a Abuja a yau Laraba.
Ya ce an ƙayyade kuɗin fom ɗin na-gani-ina-so na takarar shugaban ƙasa a kan naira miliyan 30, yayin da fom ɗin takarar kuma ya ke a matsayin naira miliyan 70, wanda jimlar kuɗin suka kama naira miliyan ɗari.
Haka kuma ya ce jam'iyar ta ƙaiyade kuɗin don ɗin takarar gwamna a kan Naira miliyan 50, inda ta ce miliyan 10 kuɗin don ɗin na-gani-ina-so, sai kuma kuɗin don ɗin takarar Naira miliyan 40.
Kuɗin fom ɗin takarar Sanata kuma Naira miliyan 20, inda za a biya kuɗin fom ɗin na-gani-ina-so, naira miliyan 3, sai kuma kuɗin fom ɗin takara, naira miliyan 17.
0 Comments