Wani mutum ya yanka matar aure da ɗiyar ta a jihar Kebbi.
Aliyu Samba
A ranar Litinin 11/04/2022 da misalin karfe 02:00 na dare, wani mai suna Idris Suleiman dan shekara 25 dan asalin garin Maradi ta jamhuriyar Nijar ya shiga gidan wani mutum mai suna Akilu Aliyu dake titin Labana a unguwar Sani Abacha Bye Pass a Birnin Kebbi, ya yi amfani da adda ya yanka matar gidan Sadiya Idris da diyarta Khadija Akilu mai shekaru 4.
Bayan samun rahoton, tawagar ‘yan sandan da ke sashen binciken manyan laifuffuka na jihar Kebbi sun gudanar da bincike kuma sun yi nasarar cafke wanda ake zargin. A yayin gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kashe marigayiyar ne saboda kiransa da dabba kuma mara amfani da tayi.
Ya kashe diyarta mai shekaru 4 da haihuwa domin kada asirin sa ya tonu bayan ta gane shi.
0 Comments