"Ni Da Iyalina Musulmai Ne." Dan wasan Barcelona Ansu Fati.

Matashin dan kwallon barcelona, Ansu Fati ya bayyana karara cewa shi da ahalinsa musulmai ne kuma suna alfahari da kasancewarsu a haka.

 “Ni da iyalina Musulmai ne. Mun yi imani. Mun yi Imani da yin addu'a da yawa. A koyaushe ina yi wa iyalina addu’a, kuma abu na Æ™arshe da na yi shi ne yi wa kaina addu’a.” Ya jaddada
 
Ya kara da cewa, "Na girma ba tare da mahaifina ba yana da wuyar gaske, Mahaifi na ya zo Spain don neman abin rayuwa a gare mu, kuma na zauna a Guinea-Bissau, ban iya ganinsa ba sai ina kusan shekaru 7 kuma na bar ƙasata don zuwa Seville." In ji shi.

"Muna da haÉ—in kai sosai, sai dai Mun sha wahala sosai. Sai dai yanzu abubuwa sun sauya cikin hukuncin Allah." Ya bayyana.
 
 "Mafarkina a yanzu shi ne in koma Guinea-Bissau in taimaka wa yaran can da abubuwa kamar ilimi, kuma in san inda nake zaune, domin in rinÆ™a tuna yadda komai ya kasance a baya." Ya shelanta

Post a Comment

0 Comments