Majalisar Dattijai Ta Bada Umarnin Ajiye Aiki Ga Duk Mai Neman Tsayawa Takara
Daga Yusha'u Garba Shanga
Majalisar dattijai ta Nijeriya ta bakin shugaban ma'aikatan ta, ta bada umarnin ajiye muƙami ga duk masu madafan iko naɗaɗɗu don samun damar shiga zaɓen 2023.
Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar ta ce wannan yana zuwa ne don bin umarnin sabuwar dokar zaɓe da shugaban ƙasa ya sanyawa hannu ta 2022.
0 Comments