Kungiyar Alheri Danko Ne Ta Raba Wa Marayu 110 Kayan Sallah Da Tallafama Kungiyoyi A Kafin Soli
Auwal Isah @ZamaniMediaCrew.
Da Safiyar ranar Larabar nan, kungiyar nan ta 'Alheri Danko Ne' ta Dakta Mustapha Inuwa, dan takarar gwamnan jihar Katsina karkashin jam'iyyar APC, ta sauka a garin Kafin Soli inda ta rabawa Marayu 110 kayan Sallah da kuma bada tallafin kudaden ga Kungiyoyi sama da guda 40.
A yayin taron, Marayun da suka kasance yara Maza da Mata wadanda suka rasa Iyaye ne kadai suka amfana da Shaddodi (ga Maza), a yayin da su kuma Mata aka raba masu Atamfofi domin su ma su yi dinkin sallah kamar sauran da ke a gaban Iyayensu.
Raba kayan dai, an yi masa tsari na za6o yara biyar-biyar (Maza 2 Mata 3) daga kowace maza6a cikin maza6u 10 na karamar hukumar Kankiya inda aka ba wa Marayu 110, sa6anin shekarun baya da ake ba wa yara 60 kacal.
Kungiyoyin al'umma maza da mata da suka haura guda 40 ne su kuma suka amfana tallafin kudade domin su gudanar da cefanen Sallah ga Iyalansu.
Kungiyoyin da aka ba wa tallafin sun hada da; 'Kungiyoyin Alheri Danko Ne' na ward-ward, da Exco-Exco sauran wasu masu ruwa da tsaki.
Sauran kungiyoyin kuwa sun hada Kanikawa, Teloli, Masu saida Shayi, Dattijai, 'yan acha6a, Matasa, Dattawa Maza da Mata da sauran kungiyoyi.
Akwai kuma Limamai da Ladanai da makaranta Alkur'ani Alarammomi da sauransu, su ma an kasafa su a cikin tsarin bayar da tallafin.
Da yake jawabi jim kadan bayan kammala bayar da Tallafin, shugaban kungiyar, Alhaji Sulaiman Garba Kafin Soli, ya yi godiya ga Allah ya ba su damar sake raba wannan abin alheri wanda kungiyar ta 'Alheri Danko Ne' ta saba rabawa tsawon shekaru uku, rabon tallafin da suke yi daga cikin aljihinsu, inda kuma ya sha alwashin ci gaba da jagorantar wannan aiki na tallafawa marayu har ma da lillinkawa saboda soyayyar da suke yi wa Mustapha Inuwa, inda ya sha alwashin kara fadada taimakon idan Allah ya kai Dakta Mustapha Inuwa ga darewar kujerar Gwamnan jihar Katsina a za6ukan shekarar 2023.
"Shekaru Uku da suka wuce muna tallafawa Marayu 60, bana mun tallafawa marayu 110." In Ji Shi
"A shekaranjiya zuwa jiya, na yi tunanin cewa mu nemo kudi su kuma kungiyoyin da muke tare da su mu yi masu wani tanadi ko da na Iccen miyar Sallah ne su Siya."
0 Comments