Kungiyar Alheri Danko Ne Ta Raba Kayan Azumi Ga 'Ya'yanta.
Daga Auwal Isah.
Kungiyar nan ta Siyasa mai suna "Alheri Danko Ne" mai rajin goyon bayan dan takarar gwamnan jihar katsina a karkashin jam'iyyar APC da taya shi yakin neman za6e, Dakta Mustapha Inuwa ta raba kayan azumi ga 'ya'yanta.
Taron bayar da tallafin kayan azumin wanda ya gudana a ranar Larabar nan 6 ga Afrelu, 2022 a ofishin kungiyar da ke Titin zuwa filin jirgi kan sabon Titin Kwado, ya samu halartar shugabanni da 'ya'yan kungiyar.
Da yake bayani a yayin bada kayan, shugaban kungiyar na jiha, Sulaiman Garba kafin Soli ya bayyana bada kayan azumin a matsayin wani wata hu66asawa ta musamman wanda kungiyar ta yi domin tallafa masu da kayan na kama azumin watan Ramadana, inda ya ba 'ya'yan kungiyar hakuri bisa ga jinkirin da aka samu ba a bada ba tun da farkon azumi, sai da har aka yi kwanaki biyar da fara azumi.
Ya ce tuntuni suna bada suna ba da irin wannan tallafi, amma wannan shi ne karon farko na ya bayyana a zahiri da zahiri.
Kafin Soli, ya kuma bayyana wannan gudumkuwar kayana abinci ga 'ya'yan kungiyar a matsayin gudummuwa wadda kungiyar ke hadawa ta taro sisi daga aljihunta, ba jam'iyya ko wani ke bayar da su ba.
"Duk wadannan abubuwan da kuke gani tun daga Masara, Gero Shinkafa, Suga... 'kungiyar Dakta Mustapha Alheri danko ce ta siya, ba jam'iyya ta bada ba. Mu ne muka rika hada kudinmu tare da shugabanin wannan kungiya; aka hada karfi da karfe aka sai wadannan kaya."
Sulaiman Garba, ya kuma bayyana irin nasarorin da kungiyar ta samu tun daga lokacin da aka kafa ta zuwa yanzu kimanin shekara biyu da rabi, inda ya ce suna fafutika tun ana cewa ba a yi, ga shi yau an wayi gari wasu su ne masu neman shigowa a cikinta ido rufe.
A yayin da yake karkare jawabi sa a taron, Sulaiman kafin Soli ya yi wa 'yan kungiyar albishir da cewa; "Kuma daga nan zuwa bayan sallah muna saon mu kira taron gangami na kananan hukumomi 34 wadanda za mu zo mu zauna da Dakta Mustapha mu gana da kungiyar alheri danko ne ya ga ayyukan da ta yi ya yi mana godiya."
An ba wa kowane 'Zone' kasonsa, 'Ward' ma da nashi kason, sannan da kuma exco su ma da nasu kason.
A yayin taro, shugabanni da 'yayan kungiyar ne suka halarta. Sai 'Yan jarida, a yayin da jami'an tsaro suka sa ido don ganin komai ya tafi daidai ba tare da wata hayaniya ko tarzoma
0 Comments