Jam'iyyar PDP ta shigar da kara kotu akan Zabukan kananan Hukumomi da akayi a ranar Litinin din da ta gaba ta

Jam'iyyar PDP ta shigar da kara kotu akan Zabukan kananan Hukumomi da akayi a ranar Litinin din da ta gaba ta 

Ahmed Badamasi Zamani Media crew

Ranar litinin din da ta gabata ne Hukumar Zabe mai zaman kanta reshen jihar katsina ta aiwatar da zaben kananan hukumomi a fadin jihar Katsina.

Sakataren Hukumar zabe mai zaman kanta reshen jihar katsina ne ya bayana yan' takarar da sukayi nasara a zaben da ya gabata, inda Jam'iyyar APC mai mulki tayi nasarar lashe Ciyamomi 33 da kansiloli 351, inda aka bayana zaben karamar hukumar Dustin-ma a matsayin Zaben da bai kamala ba.

Jam'iyyar adawa ta PDP tayi watsi da zaben inda ta bayana zaben a matsayin wasan yara, Jam'iyyar ta PDP tayi nasarar shigar da Kara kotu a babbar kotun jihar (High court) a ranar Laraba 13-04-2022.

Jam'iyyar ta PDP ta bayana ma kotu zaben bai cika ba kamar yadda doka ta tanada. 
Jami'yyar ta PDP ta bayana ma kotu a sashen Zabe na 82 na kananan Hukumomi ta 2002, an bayana a shigar da kara katu a cikin kwana goma daga ranar da aka bayyana sakamakon zabe. Wanda an bayana sakamakon zaben ne 11-4 -2022

Post a Comment

0 Comments