Daga Muhammad Inuwa Zariya
A yau litinin ne gwamnatin jihar Kaduna ta tura tawagarta ga babban masarautar karamar hukumar Igabin jihar Kaduna domin zaman tattaunawa kan samun matsayar yadda biyan harajin Gidaje da Gonaki zai biyo baya a duk fadin illahirin jihar Kaduna.
Taron wand ya samu wakilcin kwamishinan kananan hukomomi da Masarautu, da shugaban tattara haraji na jiha da shugaban kididdiga na jihar kaduna.
A zaman an bayyana duk wanda ba shi da katin zama dan kasa to ba dan jihar kaduna ba ne.
Haka nan an bayyana cewa duk kudin da za a amsa, gwamnati ba za ta amfana da ko sisi ba mutanen wajen ne za a yi wa aiki da kudin nasu.
Wakilin gwamna nasiru el'rufai ya ce, daga wannan watan kowane mai anguwa zai dunga ganin albashin shi dubu 10 duk wata kamar yadda aka fara yi a baya, saboda masu unguwanni sun fi kowane mai sarauta aiki da jin koken al'umma.
Ya ce duk wani Dagaci za a ba shi kyautar mashin sabo fil a leda saboda su dunga kewaya halin da al'ummarsu ke ciki.
Ya kara da cewa duk bakon da ya wuce kwana 180 to ya zama Dan gari sai ya biya haraji. Haka nan kuma Fulani za su biya kudin ta hannun Mai anguwan da suke a Karkashinsa.
Daga karshe ya jawo hankalin mutane da cewa a duk lokacin da suka biya harajin, to ka da su tafi; su tsaya su kar6i rasidi, in ba haka ba dole su biya wani.
0 Comments