Dan Takarar Ciyaman Na Karamar Hukumar Kankiya A Karkashin Jam'iyyar PDP Ya Zagaya Garuruwa Yakin Neman Za6e.

Dan Takarar Ciyaman Na Karamar Hukumar Kankiya A Karkashin Jam'iyyar PDP Ya Zagaya Garuruwa Yakin Neman Za6e.

Daga Auwal Isah: Zamani media crew.

Dan takarar Ciyaman a karkashin Inuwar Jam'iyyar adawa ta PDP na karamar hukumar Kankiya, Alhaji Yusuf Abubakar kafin soli ya zagaya garuruwan yankin a yakin neman za6ensa.

Yakin neman za6en nasa dai ya soma gudanar da shi ne a safiyar ranar Alhamis din nan, inda ya shafe tsawon yini guda yana gudanar da zagayen a garuruwa da kauyuka daban-daban.

Garuruwan yakin neman za6en wadanda ya zagaya a cikinsu sun hada da; 'Ward' din tafashiya/Nasarawa, Tafashiya, da Sabuwar Duniya.

Sauran sun hada da Nasarawa, Kawari, 'Yar Laya da sauransu.

Zagayen yakin neman za6en wanda ya zagaya garuruwa 15, ya samu halartar dimbin magoya baya da suka hada da dattijai, tsaffi yara da mata, manya da kanana, zagayen da ya samu rakiyar jam'ian tsaro da kuma 'yan jarida.

A jawaban da ya gabatar a mabambanta garuruwan da ya halarta, ya sha wa jama'ar yankin alwashin cewa muddin suka za6e shi, to kuwa ba zai watsa masu kasa a ido ba.

Ya ce, al'umma su ne suka neme shi da ya fito wannan takara, shi ya sa ya fito. Kuma ya bar wa Allah komai a kan yadda za ta kasance, domin sun san cewa Allah ke komi, ba wani ba.

"Ina tabbatar maku inshaAllahu ba za ku yi da na sani ba (idan kuka za6e ni."

A yayin zagayen, har wayau, ya samu rakiyar 'Yan takarkarin Kansilolin 'wards' guda biyu na karamar hukumar ta kankiya a karkashin jam'iyyarsa ta PDP, wadanda suka hada da; Sufiyanu Suleiman, da Nura Abdullahi. 'Yan takarkarin da yake gabatarwa jama'a su a yayin da duk zai gabatar da jawabi, inda yake shaida wa jama'a cewa su ne 'ya takarkarinsa a jam'iyyar adawa ta PDP a karamar hukumar ta Kankiya.

Sauran wadanda suka taya shi zagayawa a yakin za6en sun hada da; dan takarar Majalissar Tarayya Alhaji Jabiru Mukhtar Nasarawa tare da Ciyaman din jam'iyyar PDP na Kankiya, Alhaji Ibrahim Abdullahi Tafashiya.

A yayin zagayen, daruruwan magoya baya ne suka tarbe shi a garuruwan da ya je, tare da yi masa fatan alheri da cewa ranar za6e shi ne za su ba dama ya dare karagar kujerar shigabancin karamar hukumar ta Kankiya a matsayin ciyaman.

A ranar Litinin din nan mai zuwa ne 11 ga watan afrelu, 2022 za a kada za6en kananan hukumomin jihar Katsina guda 34, inda kowane dan takara daga jam'iyyu daban-daban musamman manyan jam'iyyu guda biyu; PDP da APC a yanzu suka bazama yakin neman za6en kafin ranar za6en.

'Yan magana dai na cewa, ba san maci tuwo ba sai miya ta kare.

Post a Comment

0 Comments