Ba mu da masaniya kan matakan tsaron da aka dauka a zaben kananan hukumomin Katsina — PDP

Ba mu da masaniya kan matakan tsaron da aka dauka a zaben kananan hukumomin Katsina — PDP

Babbar jam'iyyar hamayya a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, PDP, ta ce ba ta san irin matakan tsaron da aka dauka dangane da zaben kananan hukumomin jihar da za a yi a ranar Litinin ba.

Wasu 'ya'yan jam'iyyar sun koka da rashin sanar da su irin shirye-shiryen da hukumar zabe ta yi na tunkarar zaben kananan hukumomin musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Bashir Tanimu Gambo, jigo ne a jam'iyyar ta PDP a Dutsenma, ya shaida wa BBC cewa, kowa ya san jihar Katsina na fama da matsalar tsaro, inda akwai kananan hukumomi kamar 9, da a nan matsalar ta fi kamari.

Ya ce, an riga an san wadannan kananan hukumomin 9, a nan ne 'yan ta'adda ke abin da suka ga dama, kamar karamar hukumar DanMusa da Safana da Batsari da Kankara da Faskari da Sabuwa da Dandume da kuma Jibiya da wasu sassa na Dutsenma da Kurfi.
Dan jam'iyar ta PDP, ya ce," Ba maganar adawa ba ce, magana ce ta gaskiya saboda duk a fadin Najeriya kowa ya san matsalar da jihar Katsina ke fuskanta ta fannin tsaro, sannan hukumar zabe ta ki fitowa ta fada wa mutane halin da ake ciki na wasu runfunan zabe."

Ya ce, magana ta zabe magana ce ta al'umma wanda kuma suke bukatar a yi musu jawabin irin hanyoyin da za a bi wajen ba wa mutanen da ke zaune a yankunan da ke da matsalar tsaro damar kada kuri'a.

Bashir Tanimu Gambo, ya ce, ya kamata gwamnatin jihar wadda ke karkashin jam'iyyar APC, ta fito ta yi wa jama'a bayani a kan shirye-shiryen da aka yi na gudanar da zabe a yankunan da ke da matsalar tsaro.

Ya ce, yin haka shi ne zai tabbatar da cewa an ba wa kowa damar zaben wanda yake so ya zaba, don dole a yi abin da ya dace.

Wannan dai na zuwa ne a yayin da a ranar Litinin 11 ga watan Afrilun 2022, za a gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar ta Katsina.

Akwai dai kananan hukumomi 34 a jihar da kuma mazabu 361.

Post a Comment

0 Comments