An Kafa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Katsina
Babban jojin jihar Katsina, Justice Musa Danladi. |
An Kafa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓe, dana Ɗaukaka Ƙara akan Zaɓen Ƙananan Hukumomin Katsina
Babban Jojin Jahar Katsina, Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar ya naɗa Kotunan Sauraren Ƙararraki dana Ɗaukaka Ƙara akan zaɓen Ƙananan Hukumomi da aka gudanar a ranar Litinin a Jahar.
Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓen tana da kwanaki 90 domin ta yanke hukunci akan shari'ar da aka shigar a gabanta, a yayinda Kotun Ɗaukaka Ƙara ke da wata ɗaya domin domin duba hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen ta yanke akan zaben da aka gudanar.
Shuwagabanni da Mambobin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen za'a rantsar dasu a ranar Laraba a ɗakin taro na Babbar Kotun Katsina dake Katsina, da misalin ƙarfe 11 na safe.
Jojin mai Kula da Lamarin Kotunan Zaɓen, Mai Shari'a Abas Abdullahi ya bayyana haka a lokacin taron Manema Labaru a ranar Litinin.
Yace "biyo bayan zaɓen Ƙananan Hukumomi a Jahar Katsina a ranar 11 ga watan Afrilu na Shekarar 2022, da
kuma Ikon da aka baiwa Babban Jojin Jahar Katsina na Sashe 79, da 81(2) da Sashe 88(1) (2) da kuma Sashe na (3) na Dokar Ƙananan Hukumomi ta Shekarar 2002, Babban Jojin Jahar Katsina, Mai Shari'a Musa Danladi Abubakar ya Kafa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓe da Ɗaukaka Ƙara a Jahar Katsina, domin sauraren Ƙararraki, da kuma Ɗaukaka Ƙara akan Zaɓen Ƙananan Hukumomi a Jahar.
"An kafa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓen guda uku a kowace Shiyya ta Ɗan Majalisar Dattijai ta Jahar, da suka haɗa da Shiyyar Katsina, da Shiyyar Funtua da kuma Shiyyar Daura".
Mai Shari'a Abdullahi ya kuma bayyana cewa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓen na Shiyyar Katsina da Daura zasu gudanar da sauraron Shari'ar a Katsina, a yayin da ta Shiyyar Daura zata gudanar da Sauraren Shari'ar a Daura.
Ya bayyana cewar dukkanin wasu hanyoyi na Shigar da Shari'ar, za'a shigar dasu ne a Sakatariyar Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe a Katsina, domin "sauƙaƙe wahalhalu na biyan.
0 Comments