Adamawa - Jam'iyyar PDP ta lashe baki É—aya kujerun Ciyamomi da Kansiloli a faÉ—in kananan hukumomi 21 na jihar, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Jam'iyyun siyasa d aba su gaza 18 ba ne suka tsayar da yan takara a zaɓen kananan hukumomin wanda aka gudanar ranar Asabar.
Da yake sanar da sakamakon zaɓen ranar Lahadi a Yola, babban birnin jihar Adamawa, shugaban hukumar zaɓen jiha mai zaman kanta (ADSIEC), Mr. Isa Shettima, ya ce APC da PDP ne kawai suka ɓarje gumi a zaɓen ciyamomi.
Shettima ya ce:
"Daga cikin jam'iyyu 18 da suka nuna sha'awa, Jam'iyyar PDP da APC ne kawai suka gwabza a zaɓen shugabannin kananan hukumomi."
Ya APC ta ji wannan shan ƙasa da ta yi?
Kakakin APC-Adamawa, Abdullahi Mohammed, da aka tuntuɓe shi, ya bayyana cewa babu wani zaɓen da aka gudanar da jihar, domin ba'a kai kayan zabe wasu runfuna na ba sam.
Ya ce a APC na cigaba da tatara kwararan shedun aikata maguɗi a zaɓen kuma zata sanar da matsayarta ba da jimawa ba.
Ya ce:
"Ba wani zaɓe da aka gudanar a baki ɗaya yankunan kananan hukumomi 21 dake faɗin jihar. Wasu tsirarun jami'an gwamnati ne suka zauna suka tsara sakamakon da ransu ke so."
0 Comments