A Gobe Litinin 'Yar Marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam, Za Ta Bude Tafsirin Mata A Jihar Kano
'Yar marigayi Sheikh Ja'far Mahmoud Adam, Malama Zainab ja'afar, zata Fara Gabatar da tafsirin azumi na Mata, a massalacin Juma'a na Usman Bn affan Dake kofar Gadon Kaya a birnin Kano.
Ana gayyatar 'yan uwa musulmi Mata, zuwa bude wanan tafsiri da za'a farashi daga Gobe litinin 10 ga Ramadan daga karfe 9 na safe zuwa karfe 12, Kuma tafsirin zai cigabada gudana har zuwa karshen Ramadan.
0 Comments