Mutane 6 sun mutu, a yayinda Mazauna Shimfiɗa suke gudun hijira saboda janye masu Sojoji

Mutane 6 sun mutu, a yayinda Mazauna Shimfiɗa suke gudun hijira saboda janye masu Sojoji

Rahotanni sun bayyana cewa Mutane 6 wanda yawancin su yara ne ƴan Asalin garin Shimfida dake Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jahar Katsina, suna gudun hijira a dalilin abinda suka bayyana a matsayin "cire Sojoji ba tare da sanar dasu ba a yankin.

Wannan mummunan lamari ya haddasa mutane da yawa sun bar mahallin su zuwa wani wuri sakamakon tsoron kawo hare-haren ƴan bindiga.

Mazaunan sun shaidawa Daily Trust a ranar Laraba da daddare cewa, Motocin da aka ajiye na sojoji a yankin, sun bar wurin da suke na wani lokaci.

Shimfida ta kasance tana kusa da Dajin Dumburum inda Manya-manyan Kwamandojin Ƴan bindiga suke gudanar da ta'addancin su a Zamfara da Jahar Katsina suna ɓoyewa.

"Sojojin suna a wannan wurin na tsawon Shekaru 7, domin Shimfida tana ɗaya daga cikin garuruwan da ƴan
bindiga suka fara kai hari a farkon fara ta'addanci, shekaru bakwai da suka wuce.
"Sojojin ya kamata su bamu a ƙalla kwanaki biyar, domin mu bar wurin, amma abun baƙin ciki sun kwashe kayan su, sun barmu a dai-dai lokacin da ƴan bindiga ke kai hari.

"Da nake magana daku yanzu, tsofaffi Maza da Mata, da ƙananan yara, suna guduwa domin barin garin, kuma a halin yanzu gawar ƙananan yara shida an same ta akan hanya," inji shi.

Wani Mazaunin garin yace ya zama abin gaggawa, kuma ya zama dole su bar garin, saboda ƴan bindigar suna jin haushin mazauna ƙauyen a dalilin Kasancewar Sojoji a garin.

Duk wani yunƙuri domin jin dalilin cire Sojojin daga Barikin Soji na Katsina bai samu ba.

A ɓangaren shi, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Katsina SP Gambo Isah yace "idan har sojoji zasu bar garin, su ya kamata suyi magana akan dalilin, amma ba Ƴan Sanda.

Post a Comment

0 Comments