JI DA GANI DA IDO: Kamfanin Sadarwa na Zamani ya fara gudanar da Aikinsa a Birnin Katsina...

JI DA GANI DA IDO: Kamfanin Sadarwa na Zamani ya fara gudanar da Aikinsa a Birnin Katsina...
A ranar Alhamis 3 ga watan da muke ciki na Maris, tawagar Kamfanin Zamani Media Crew katsina, a karkashin wani sabon shiri da zai dunga zo maku sau biyu a mako a kafar sadarwa ta Zamani Media Crew, mai suna "HATSIN BARA" sun zagaya Birnin Katsina, domin Tattaro wasu batutuwa da al'umma na ciki da wajen jihar Katsina suke so suji kuma su gani, Kamfanin yayi rangadin ne bisa tsari, da idan kuna bibiyar shirin, zai zamar maku Jihar Katsina a tafin hannun ku. Wato bako da É—an gari, zai san Katsina' Al'adun mutanen Katsina, sana'o'in su da mu'amula. Shirin bai tsaya a nan ba ya leka wasu daga cikin muhimman Ayyuka da Gwamnatin Katsina take yi a cikin Birnin, kuma sunji ra'ayin Al'umma dangane da Ayyukan na ci gaba. 
Tawagar Zamani Media Crew sun yi dirar mikiya a Babban titin Kofar Kwaya, inda Gwamnatin Katsina take gudanar da Aikin Titin Æ™arÆ™ashin Æ™asa wato (Underpass  way) Wakilin Zamani Media Crew sunga an Datse hanyar da ta taso daga Titin ATC zuwa kofar kwaya da wadda ta taso daga Babban titin Kasuwar Katsina zuwa kofar ta kwaya da wanda ya taso daga Masallacin Mangal zuwa Shatale-talen Kofar kwayar, sana suka tattauna da 'yan Kasuwa da mazauna Unguwar ta Kofar kwaya akan yanda suke kallon Aikin da yanda ya shafi kasuwancin su. Da yake Titin shine ya haÉ—a kusan Dukkanin Manyan makarantun gaba da Sakandire na Katsina, Zamani Media Crew sun samu tattaunawa da ÆŠalibai.
Daga nan kuma sai tawagar Kamfanin yaɗa labarai na Zamani Media Crew suka karkata suka bi Titin da ya rage wanda Ma'aikatan basu datse ba saboda sauƙaƙa zirga-zirga, wato Titin Yahya Madaki zuwa Kofar Kaura, inda anan tuni aiki yayi nisa, inda tawagar tamu taga yanda ake Aiki babu kama hannun raggo. Duka wannan Rangadi mun naɗeshi a cikin faifan Video 📸 da na Sauti, wanda kai tsaye zaku samesu a cikin tashoshin mu na YOUTUBE da kuma Radio 📻.
Shirin Hatsin bara, bai tsaya nan ba ya kutsa cikin wata shahararriyar Kasuwa ta 'yan wayoyin hannu, inda bayan naɗo maku yanda Al'umma ke hada-hada a kasuwar mun samu Zantawa da Tukur Isa Mani, Shugaban Kungiyar masu sana'ar wayoyin hannu na jihar Katsina, inda muka naɗe maku tattaunawar tsaf cikin salama a Faifan Video 📸, da Sauti na Radio 📻.

........Kasuwar da ake kira Tsaitsaye, ta Matse kuma ta shiga lungu..............

Gwamnatin Katsina taba 'yan Kasuwar Katon fili domin ginawa da komawa domin su wala. Ina aka kwana...?

......Minene Alfanun Shiga Ƙungiyar masu saida wayoyin hannu.....?

.......Shin ko wane tsari da tsaro sukayi domin kuɓuta daga faɗawa cinikayya da ɓarayi masu kwamushe wayoyin mutane...?

Duka waɗannan tambayoyin Shugaban ƙungiyar ya amsa su.....Amma a zahiri, wato a cikin Faifan Video da Audio, sai muce ku kasance a cikin shirin Hatsin Bara da zai dunga zo maku a Duk mako a tashar mu ta YOUTUBE da kuma Radio 📻

Ko a sauran kafofin mu na sada zumunta, Idan kuka lalubo Zamani Media Crew Katsina. Daga Kasuwar masu saida wayoyin hannu wato kasuwar Tsaitsaye sai muka garzaya a Unguwar Modoji.
Unguwar Modoji' inda ake ɗaukar shirin Film ɗin Lu'u lu'u, Fim mai dogon Zango da Kamfanin Kanywood Exculusive ke shiryawa, inda muka tattauna da Jariman Film din da ma'aikatan shirin. Mi shirin Film ɗin ya ƙunsa...? Shima dai ku kasance da Zamani Media Crew Katsina a www.zamanimediacrew.com.ng

kuma zaku iya sauke manhajar mu a wayoyin hannun ku da suka haÉ—a dukkanin shafukan mu, inda zaku ji ku gani. .............Zamani akan zamani, Duniya Busa tafin ku. Rahoto: data Aminu Salisu Tsagero

Post a Comment

0 Comments