Dalilan Da Suka Sanya Nike Son In Gaji Masari A 2023 — Inji Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina

Dalilan Da Suka Sanya Nike Son In Gaji Masari A 2023 — Inji Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina

Dalilan da suka sanya nake Son in Gaji Masari — Cewar Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina

A matsayin wani ɓangare na shirye-shirye domin tunkarar Babban zaɓen Shekarar 2023, Sakataren Gwamnatin Jahar Katsina (SSG) Mustapha Muhammad Inuwa ya zanta da gidan Jaridar The Nation

Tambaya: Kana son ka zama Gwamnan Katsina. wane irin dangantaka ke tsakanin ka da muhimman mutane Masu ruwa da tsaki a Jaha.
Amsa " a waje na, inada maƙurar kyakkyawar dangantaka ga dukkanin mutumen da muka haɗu. Muna da Fahimta da dangantaka mai ƙarfi. Inada abokanai ƴan siyasa, wanda muka yi aiki tare ko kuma bamu yi ba, Ni babbar matsala ta shine, ina tsayawa tsayin daka ga dukkanin abinda nayi imani dashi. Da zaran na fahimci wannan shine abinda ya kamata nayi, kuma na yarda, to zan tsaya akan shi. Kuma bazan damu da wanda zai zage Ni ba, musamman idan ya kasance abinda ya shafi Al'umma ne gaba ɗaya.

Kamar yadda na faɗa, nayi aiki a Jahar nan, kusan kowane ɓangare, nayi aiki a sassan Ma'aikatun Jaha, nayi aiki a Ma'aikata, kuma na zama Sakataren Gwamnatin Jaha. Na kuma yi aiki a ofishin Jam'iyya na Jaha. Mutane sun sani, da zarar na tsaya akan abu, to zan tsaya ne aka shi. Kuma ina yin bakin domin hana abinda nake ganin Ni kaɗai ya shafa, koda wa ya shafa, ka gane? Bari in baka wasu misalai guda biyu.

A lokacin da ina Malamin Jami'a, Mata ta Ɗaliba ce. Ina tunanin sau biyu tana faɗi takarda ta, kuma har yanzu bana dana sanin yin haka. A lokacin da ina Kwamishinan Ilmi, sau biyu ina zuwa Makarantar ta, ba tare da na faɗa mata ba zanje. Na barta a gida, kuma na bata takardar gargaɗi saboda tazo a Makare.

Ta kasance Mataimakiyar Shugabar Makarantar Shargalle, an bata muƙamin Shugabar Makarantar Sakandire, kuma aka tura ta Sandamu wanda nesa ne daga Katsina. Kuma a lokacin da ta gaya mani, na maida mata amsa cewa, dole kije aikin ko kuma ki ajiye, domin bazan yiwa kowa magana ba akan tura ki da aka yi a can. To don haka, akwai abubuwa da dama da mutane suka yi imanin cewa, bazan taɓa yi ba, shiyasa zasu ji bari su nemi wanda zai yi masu yanda suke so, wanda zasu rawar gaban su, wanda Ni kuma bazan yi ba.

Tambaya: Minene matsayar ka akan shirin miƙa mulki na shiyyoyi, ma'ana na karɓa-karɓa?

Ka gani, a wannan lokacin da nake magana da kai, ban taɓa tattaunawa da wani cewa Inason zama Gwamna ba. Dukkanin abubuwan da kake gani da kuma Ji, lissafi ne na mutane waɗanda suka ga cigaba ta fuskar siyasa a Jahar Katsina. Mutane suna duba abubuwan da muka yi a baya, da abinda zamu iya a siyasance musamman a lokacin zamanin Marigayi Umaru Musa Ƴar'adua, inda nayi aiki a wurare guda huɗu.

Daga Janar-Manaja zuwa Shugaban Ruƙo na Ƙaramar Hukuma, zuwa Kwamishinan Ilmi, zuwa Sakataren Gwamnatin Jaha. Sai na shiga jami'yar hamayya, bayan na samu matsala da Gwamnatin lokacin ta PDP ƙarƙashin Shema, da kuma Shugaban Jam'iyya dana riƙe, har ya zuwa yanzu mutane na lissafawa ne akan abubuwan da mukayi.

Duk sunyi amanna cewa mun cancanta muyi Mulkin, domin ban taɓa tattaunawa da wani, saboda dalilai guda biyu. Na ɗaya, nayi imani muna cikin Gwamnati, an zaɓe mu wa'adi na biyu na shekaru huɗu, a wajena wannan shiya kamata mu duba, shiya kamata ace mun maida hankali, mi zamu yiwa Al'ummar Jahar Katsina.

Na biyu a matsayina na ɗan Jam'iyya, na amince da iko na Jam'iyya, nayi imani akan dokokin Jam'iyya. Abinda muke yi shine mu sanya Jam'iyyar a tsari mai kyau. Kasan mun fara daga Matakin Mazaɓu zuwa na Ƙaramar Hukuma. Munyi zaɓen Shuwagabannin Jam'iyyar na Jaha, yanzu kuma muna jiran zaben Shuwagabannin Jam'iyyar na Ƙasa inda zamu kasance muna da dukkanin Shuwagabanni daga matakin mazabu zuwa na Ƙasa. A wajena sai an kammala sannan zamu fara magana akan zaɓe, wanda zaizo a Shekarar 2023. Shiyasa har yanzu ina kallo. Ina kuma sauraren mutane. Amma muna jiran lokacin da ya kamata mu shiga haka. Kamar yadda nace mu jira muga farkon Shekarar 2022.

Tambaya: Yanzu zaka yi takara, ko ba zaka yi ba?

Wannan wani abu ne mai wahala da zan faɗa. Mu jira muga lokaci yazo, idan yazo kamar yadda nace, muna da hanyoyi, muna da shugabanci a Jaha , muna da shugaba wanda shine Gwamna. Ni bana tsoron tsayawa takara. Babu wani abun wahala, domin na jagoranci Jam'iyyar an samu nasara a Shekarar 2014 a matsayina na Shugaban Jam'iyya. To ba wani abu bane mai wahala. Dukkanin abinda nake cewa, mubi hanyoyi, kada mu ɓata aikace-aikacen Gwamnati, kada mu dami gwamnati, matsalar shine a yanzu idan na fito a matsayina na Sakataren Gwamnatin Jaha, kuma akwai yiwuwa Mataimakin Gwamna zai yi takara, kuma ƙila akwai alamar wasu zasu fito takara. To ta yaya zaka ga irin Gwamnatin da zamu yi? Ka fahimta?

Mu jira zuwa lokacin da jam'iyya zata ce muyi, sai mu kalli abin, amma kamar yadda nace mutane zasu cigaba da abinda suke yi sosai, dukkanin abinda muka ce muna gani kamar Fastoci, banoni, a Kafafen Sadarwa na Zamani, dukkanin su mutane keyi, wanda suka amince zamu iya. Suna da manufar su cewa zamu iya. Kuma Bama cewa zamu watsa masu ƙasa a gwuiwa, amma muyi haƙuri, har zuwa lokacin da ya dace.

Mutane suna da damar suyi abinda suke so, bamu gaya masu su faɗa hakan ba, domin wasu ma har ziyartar mu suke yi, amma dai lokaci bai ida ba.

Tambaya: A lokacin da kake cigaba da jiran lokaci, kana da abunda ka sanya a gaba, abubuwan da kake so ka cimmawa, ka fito dasu? 

Ka gani, dagaske, idan akwai wani dalili da zai sa mu fito da hakan, zamu fito, kuma mu shiga a gudanar da lamarin saboda na amince cewa muna da abubuwa da dama da muke son muga mun magance da dama, wanda muka amince cewa sune matsalolin dake damun mu a Jahar Katsina, musamman
ɓangaren ilmi, rashin aikin yi ga Matasa, matsalar tsaro, a wurina musamman wajen tattara kuɗaɗen shiga.
Nayi imani cewa, akwai abubuwan da zamu iya, amma abinda zamu yi da fahimtar Al'umma, dole mu canja yanda muke abubuwa a shekaru da dama da suka gabata, kuma bama samun abinda muke so a dukkanin tsawon shekarun, to dole ka canja takun ka.

Bazai yiwu ka riƙa yin abu ɗaya ba, kuma kayi tunanin zaka samu sakamako masu yawa. Ina tunanin zamu amince mu shiga, domin munyi imanin cewa zamu kawo hanyoyi da dama, da zasu inganta abubuwan da muka kasance muna yi.

Muna Son mu canja abubuwa a wani ɓangarorin. Dole mu canja yanda muke yin abubuwa. Kagani, dole mu wayar da kan Al'umma, Dole mu sanya su fahimci cewa, Gwamnati ba zata iya yiwa kowa abinda yake so ba a lokaci guda. Mu a matsayin mu na Al'ummar Jahar Katsina, muna da hanyoyin da zamu bada gudunmawa musamman a ɓangaren kuɗaɗen shiga. Idan muka dubi Katsina, tana ɗaya daga cikin Jahohin da suka dogara kacokan akan Gwamnatin Tarayya, kuma wannan bazai ɗore ba.

Muna kallon matsalolin, domin mun zama Jaha mai Albashi kaɗai. Abinda muka samu shine kaɗai zai isa mu biya Albashi, da yin wasu abubuwa kaɗan, muna da hanyoyin da zamu iya samar da kuɗaɗe domin magance abubuwan da Al'umma suke so. Muna da yara da dama waɗanda basa a Makaranta. Makarantun mu sun cika maƙil. Da yawansu sun lalace. Da yawansu basu da isassun Malamai, da Kayayyakin koyo da sauran su.

Ilmi shine mabuɗi ga dukkanin wani cigaba a Duniya. Domin mu magance wannan matsalar, koda mun amince duka kuɗin da suke zuwa daga Gwamnatin Tarayya ya shige a ɓangaren ilmi, bazaka iya komai ba. Wannan wani ɓangare ne dake da mutane da yawa, muna da mutane Miliyan 8, kuma suna ƙaruwa, a shekaru kaɗan masu zuwa, adadin zai ninku.

To dole mu kalli yanda muke samun kuɗaɗe duk da basu isa. Domin idan ka duba matsalar tsaro. Yana gurgunta tattalin arziki a Jahar. Dole mu magance hakan. Mun faɗi haka da dama ga Jami'an tsaro. Muna fata kafin shekarar 2023, matsalar tsaro za'a magance ta, kuma muna fata zuwa Babban zaɓe na shekarar 2023 aka gudanar dashi, sabuwar Gwamnati ta karɓa, matsalar zata zama tarihi. Amma idan akwai wani abu, to zamu kalli Al'umma, domin muga mi zamu yi mu kawo ƙarshen matsalar gaba ɗaya.

Abinda muke samu, duk kullum yana ragewa, abine mai mahimmanci. Dole ka magance hakan. Dole mutane su fahimci cewa muna da ƙudirin magance wannan matsalar. Sai ya zamanto zaka iya magance wannan matsalar, sannan zaka kalli wasu abubuwan. Babu abinda zaka iya yi ba tare da kuɗi ba, kuma bazaka cigaba da ɗaukar bashi ba, inba haka ba, zaka kai lokacin da bazaka iya ɗauka ba, domin bazaka iya biya ba. To idan ya zamanto ka ƙure abinda kake sa rai, a ƙankanin lokaci, babu wanda zai baka komai kenan.

Tambaya: Wasu mutane suna cewa baka da kyakkyawar alaƙa da Hamshaƙin Ɗan Kasuwar nan Alhaji Ɗahiru Barau Mangal?

A'a inada kyakkyawar alaƙa dashi. Tunda muka fara nasan irin rawar daya taka kafin wannan Gwamnati ta hau karagar mulki. Muna da kyakkyawar alaƙa dashi. A gurina bana tunanin muna da wata matsala tsakanina dashi. Kamar yadda nace, ko waye ko kuma dukkanin wata dangantaka dake tsakanin mu, ina Son mutane su zamanto suna da ra'ayin Jahar, ba nasu ba, da suke dashi a zuciyar su. Bazan goyi bayan kayi abinda nayi imanin cewa, zai hana cigaban Jahar nan, ko kuma zai shafi mafi yawan Mutanen Jahar nan, ko ya girman ka yake.

Wannan ne ya sanya iyalai na basa zuwa wajen aiki na, duk yanda muke da dangantaka. Babu wanda ke zuwa wajen aiki na, kuma sun sani. Idan kazo zasu gaya maka, je ka ganshi a ofishin sa. Wannan shine abinda aka amince, bamu da hannu akan haka. a gareni banda nadama akan haka. Gaskiya bana nadama. Idan wannan dalilin zai sanya bazan zama Gwamnan Jahar Katsina ba, bazai dame ni ba. Idan saboda haka mutane suka ga, bazan zama Gwamna ba, bazai dame ni ba. Bana Son Gwamna don wata manufa tawa, bazai zama ina neman Gwamna ba domin ra'ayin kaina. Kawai dai nayi imani cewa, muna da abinda zamu iya bada gudunmawar mu domin cigaba a Jahar Katsina.

Tambaya: Daga Ƙarshe, minene ra'ayin ka, akan cewa Shitu bai dawo ba a matsayin Shugaban Jam'iyya, musamman saboda dalilin tsarin karɓa-karɓa?

Amsa: Wannan shine wurin da mutane suke kuskure. Bari in gaya maka wani abu, wannan wani ilmi ne na haƙiƙa. A lokacin da muka zo a Shekarar 2014 a matsayin Jam'iyya, daga cikin mutane 26 cikin mambobin jami'iyyar, nine mutum da zaka iya kallo kace na cika ɗari bisa ɗari na Masari ne. Dukkanin su wasu suka bada su. Kodai ya kasance Sadiq ko Hadi Sirika, Audu Soja, ko tsohon Shugaban Hukumar tsaro ta Farin Kaya ta SSS Sada Ilu. Ko a ƙananan Hukumomi haka abun yake. Ƙaramar Hukumar Ƙafur, wadda itace ta Gwamna, tsarin Jam'iyyar ba nashi bane. Shiyasa nake mamaki, in kalli mutane inyi dariya idan suna magana akan tsarin Jam'iyya.

Nace, ba kowane lokaci zai kasance komai naka ba. Ban ga wani da yayi tsarin Jam'iyya kuma tayi mashi aiki ba. Masari ya kada wasu masu neman Gwamna a Jaha ko a Matakin Ƙaramar Hukuma. Mun zo da Mallam Shittu, kuma dangantakar mu bata siyasa kaɗai bace ba. Ba zaka iya cewa saboda shine Shugaban Jam'iyya, mutane na cewa zanyi takara, sai kuma mu datse dangantakar, ba zamu riƙa ganin juna ba.

Yanzu da yake Sakataren Jam'iyya. Ina fatan sun gamsu ko. Yanzu sai suji daɗi, tare da alakanta nasara ko akasin ta ga wani. Nayi imani akan abinda Allah ya Ƙaddaro zai faru ga bawan sa. Ko Mallam Shittu yana ofishin sa ko baya nan, ba shine abun tambaya ba. Bayan haka wake da tabbacin cewa zamu rayu muga shekarar 2023? Idan ka duba tarihin siyasar wasu mutanen, zakaga inda tsarin Jam'iyya Bama a buƙatar sa, musamman ta fuskar zamo wa Ɗan takara, ko kuma abinda ya shafi wata kujera. Majiya: The Nation

Post a Comment

0 Comments