A fara duban watan Sha'aban a gobe, Sultan ya umarci Musulmai
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, SultanSa'ad Abubakar ya umarci Musulmai a faɗin ƙasar nan da su far duban watan Sha'aban 1443AH da ga gobe Alhamis.
Watan Sha'aban shi ne na takwas a jerin watannin Musulunci, wanda da ga shi sai watan Ramadan.
Sultan ya bada umarnin ne a wata sanarwa da Farfesa Sambo Junaidu, Shugaban Kwamitin Shawarwari na Harkokin Addini na Masarautar Sokoto, ya sanya wa hannu a yau Laraba.
Ya ce a na sanar da al'ummar Musulmi cewa gobe Alhamis, 29 ga watan Rajab, wacce ta zo daidai da 3 ga watan Fabrairu, ita ce ranar da za a fara duban jaririn watan Sha'aban 1443 AH.
"Sabo da haka sai Musulmai su fara duban jaririn watan Sha'aban a gobe kuma duk wanda ya gan shi ya kai rahoton zuwa ga Hakimin ko dagacin ko mai unguwa mafi kusa domin ƙarin bayani,"in ji Sultan.
0 Comments