Zan Cika Alkawuran Da Na Yi Wa ASUU -Buhari




Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya na kan bakanta na cika alkawuran da ta yi wa kungiyar malaman jami'a ta kasar, (ASUU), domin kare aukuwar yajin aiki da haifar da cikas ga harkokin karatu tare kuma da inganta samar da kudi ga makarantu.


Shugaban ya yi alkawarin ne a ranar Talatar nan a lokacin da yake karbar ziyarar membobin majalisar wanzar da zaman lafiya tsakanin addinai (NIREC), a Abuja, karkashin jagorancin shugabanninta na hadin guiwa, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, da shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN, Rabaran Dr. Samson Olasupo Ayokunle.

Da yake yaba wa shugabancin majalisar ta hadin kan Musulmi da Kirista a kan shiga tsakani a batun yajin aikin kungiyar malaman jami'o'in na tsawon shekara, Shugaban ya ce ba wata kasa da ke nufin kanta da alheri da za ta yi watsi da harkar iliminta.

Shugaba Buharin ya bukaci majalisar a ganawarta ta gaba da ASUU da ta nuna wa kungiyar cewa gwamnati ta dauke su da kuma aikin da suke yi wa kasar da muhimmanci, amma kungiyar ta yi la'akari da kalubalen tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Post a Comment

0 Comments