Yaro Mai Shekaru 14 A Duniya, Ya Yi Sanadiyar Kashe Kansa A Bauchi

Yaro Mai Shekaru 14 A Duniya, Ya Yi Sanadiyar Kashe Kansa A Bauchi

Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar wani yaro matashi ɗan shekara 14 a duniya, wanda ya kashe kansa a ƙaramar hukumar Ningi.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakil, wanda ya tabbatar wa BBC da faruwar al’amarin, ya ce yaron ya kashe kansa ne ta hanyar rataye kansa a wani kangon É—aki.

Mahaifin yaron ne ya sanar da 'yan sanda game da lamarin da ɗansa ya jefa kansa. Sannan ya shaida cewa, yaron yana fama da rashin lafiyar ƙwaƙwalwa da daɗewa.

“Bayan sanar da 'yan sanda, nan take jami'anmu suka tafi inda al’amarin ya faru, kuma aka É—auki yaron zuwa babbar asibitin Ningi amma aka tabbatar da ya mutu.”

Rundunar 'yan sandan Bauchi ta ce tana cigaba da ƙaddamar da bincike, domin gano dalilin da ya sa yaron ya kashe kansa.

Post a Comment

0 Comments