Daga Wakilinmu
Kasantuwar yadda halin tsaro ya koma a kasa baki daya gwamnatoci suka bazama wajen kirkiro hanyoyin magance matsalolin ido rufe.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin dake fama da matsalar tsaro a kasa musamman karamar hukumar Giwa da ta yi iyaka da jihar Neja da Katsina masu kalubale a harkar tsaro tsudum babu ji babu gani.
Karamar hukumar Giwa ta zama abin tausayi sakamakon halin da ta shiga a wannan lokacin.
Bincike ya tabbatar da babu wata rana da za a wayi gari ba tare da jimamin farmakin yan ta'addan daji ba a dukkan yankunan dake karamar hukumar ta Giwa.
Idan mai karatu bai manta ba a kwanaki kadan baya aka wayi gari da kashe mutane masu yawan gaske ciki harda Basaraken yankin duk da kokarin da jami'an tsaro ke yi a wannan yankin.
Abin tausayi shi ne yanzu haka babu wani dake barci hankalinsa kwance a fadin karamar hukumar ta Giwa. Bisa haka ne gwamnatin jihar Kaduna ta dauki matakin gaggawa a bangarenta don shawo kan wannan bala'in.
Gwamnatin jihar ta Kaduna karkashin jagoranci Gwamna Ahmed Nasiru El-Rufa'i ta dauki sabbin matakai na kirkiro wani sashi na tsaro da ake kira da KADVS.
Wannan runduna tana taka rawar gani matuka a sashen tsaro birni da kauye. Sun zama na gaba a bangaren tunkarar 'yan ta'adda a sako da lungu na fadin kananan hukumomin jihar ta Kaduna.
Hakan kuma ya samo asali ne sakamakon alkawari da Gwamnatin jihar ta yi masu kafin shigar su wannan aiki mai hadarin gaske.
Daga cikin alkawarin da Gwamnatin jihar ta yi masu sun hada da ba su hakuri na rushe tsohuwar kungiyarsu ta da wato 'Yan Banga ko 'Yan Sintiri ya zuwa KADVS. Abu na biyu shi ne ba su tallafi da zai taimaka masu ta hanyar kula da iyalansu yayin da suke fagen fama (dauki ba dadi) da barayi a daji.
Wannan alkawari da gwamnatin jiha ta yi masu yasa matasa masu jini a jika sun bayar da hadin kai dari bisa dari don kare rayuka da dukiyoyin al'umna a duk inda suke kuma a duk inda aka tura su aiki.
Abin takaici da tausayi shi ne duk da kokarin da wadannan matasa suke yi wajen kare rayukan al'umma a cikin dare da rana bai sa an cika masu alkawarin da aka daukar ma su ba .
Bisa haka ne rundunar ta koka matuka ga manema labarai akan yadda aka maishe su kamar jakuna duk da sayar da rayuwarsu da suke yi dare da rana.
Hakan yasa suka nuna bakin cikinsu tare da mika kukansu ga mai girma Gwamnan jihar ta Kaduna Malam Ahmed Nasiru El-Rufa'i da ya taimaka masu akan wannan lamarin.
Matasan sun roki Gwamna da ya binciki lamarin domin abin na cin masu tuwo a kwarya ganin yadda suke artabu da barayi babu dare babu rana. Suka ce a halin yanzu duk da fatattaka da gumurzu da suke faman yi tsakaninsu da masu garkuwa da mutane a yankin na karamar hukumar ta Giwa to garin rogo ma ya fi karfinsu.
Matasan suka ce ga shi an ce masu babu damar mutum ya ce ba ya yin aikin bisa horo da aka ba su na sarrafa makami, yanzun haka abincin da za su rinkaci sai sun roka wanda mutane suka ce hakan a ganinsu bai kamata ba ga jami'in tsaro.
Bugu da kari sun roki Gwaman da ya zama mai binciken wannan lamarin don magance matsalar cikin gaggawa.
Suka ce su ma suna son ransu kishin kasa yasa suka bar matansu da yaransu suka fito don kare kasarsu da jama'arta amma gashi ana masu rikon kora da hali bayan an horar da su yadda ake sarrafa makami, suka ce me ake so su zama?
Karshe sun yi kira da babbar murya cewa duk wani mai hannu a cikin hana su dan alawus dinsu to ya yi wa Allah da Annabi ya tsusaya masu, idan aka saurare su za su sami kwarin guiwar ci gaba da aikin na su. Kuma sun tabbatar da cewa Gwamna zai share masu hawayensu
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kwamishinan tsaro na cikin gida Mista Samuel Aruwan don jin ko ya ya lamarin yake ganin cewa yana bakin kokarinsa game da tabbatar da tsaro a fadin jihar Kaduna ta wayar salula kafin hada wannan rahoto, amma har hada wannan labarin ba mu ji daga gare shi ba.
0 Comments