SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Ma'aikatar ayyuka, sufuri da gidaje ta Jihar katsina na sanar da Al'ummar Jihar katsina, musamman masu abubuwan Hawa cewa saboda aikin gina gadojin kasa na kofar kaura da kofar kwaya da gwamnatin Jihar ke aiwatar wa, idan Allah ya kaimu Ranar 23/02/2022.
Kamfanin da ke gudanar da aikin zai fara rushe kofar kwaya don fara aiki a wannan bangaren. Don haka ne ake baiwa jama'a shawara cewa daga ranar Laraba su kaucewa Amfani da hanyar shatale-tale na kofar kwaya.
A madadin haka ana iya amfani da wadan nan hanyoyin Kamar haka:-
Wanda ya fito daga Dutsan-ma yana so ya je kofar yandaka zuwa cikin gari, Zai iyabi ta shatale-tale na sabuwar tasha, yabi ta abatuwa, rahama, masallacin Mangal zuwa kofar yandaka. Haka zalika shima Wanda ya fito daga kofar yandaka yana so zai dawo hanyar Dutsan-ma zai yi amfani da hanyar.
Haka zalika wanda wanda ya fito daga Sabon layi, tsohuwa tasha, ATC zaije Dutsan-ma, yana iya bi ta cikin filin makarantar ATC ya dawo ta tanki ya bullo dai dai tayoyi akan titin murtala Muhammad zuwa junction na masallacin Mangal zuwa shatalai talai na sabuwar tasha.
Gwamnatin tana Kara baiwa jama'a hakuri bisa ga Dan lokacin da za'a dauka na rufe hanyar da za'ayi, tare da fatan za'a ba gwamnatin da ma'aikatan kamfanin cikakken hadin kai don a samu sukunin tafiyar da aikin cikin kwanciyar hankali.
0 Comments