Nice Ta Yi Waje Da PSG Masu Rike Da Kofin French Cup


Paris St-Germain ta gaza kare kambunta na gasar kofin kalubalen Faransa, wato French Cup a ranar Litinin , bayan da Nice ta doke ta a bugun daga kai sai mai tsaron raga.

Bayan da aka tashi wasan canjaras babu ci ne, sai Nice ta lashe wasan da ci 6-5 a bugun fenariti.

Mai tsaron raga  Marcin Bulka,  wanda Nice ta dauko aro daga PSG ne ya kama kwallon da ta kawo karshen fatan PSG na lashe kofin.

ya hana kwallon  Xavi Simons shiga raga, lamarin da ya kai nice matakin daf da kusa da karshe, kuma za su fafata ne da Marseille.

Wannan rashin nasarar, koma baya  ne ga kocin PSG Mauricio Pochettino, wanda ya fito da tawaga mai karfin gaske, ciki har da Lionel Messi da zummar lashe wasan.

Post a Comment

0 Comments