Ministar Abuja Ta Gamu Fushin Matasa
Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wasu fusatattun Matasa sun yi wa karamar ministan babban birnin tarayya Abuja, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu, ihu a yayin da ta ke mika satifiket ga zababbun shugabannin kananan hukumomi a Abuja.
Kwamishinan zabe a babban birnin tarayyar, Alhaji Yahaya Bello, ya mika takardun shaidan lashe zabe ga zababbun shugabannin a taron da manyan yan siyasa suka halarta.
Wasu magoya bayan jam’iyya sun datse jawabin Tijjani a lokacin da ta shawarci Hukumar INEC ta gano hanyar da mutane za su yi zabe da takarda idan na’urar lantarki na zabe ta samu matsala.
Magoya bayan sun rika ihu suna cewa ‘Karya ne ba ma so’. Ministan ta yi kokarin ta kwantar wa mutanen hankali amma suka cigaba da yi mata ihun ‘ba ma so’.
Sanata Philip Aduda, mai wakiltar Abuja a Majalisar Wakilai na Tarayya, ya fice daga wurin taron cikin fushi.
0 Comments