Matasa da dama a Najeriya sun bazama a shafukan sada zumunta

Matasa da dama a Najeriya sun bazama a shafukan sada zumunta inda suka dinga mayar wa jagoran jam'iyya mai mulki ta APC Bola Ahmad Tinubu martani, kan kalamansa da ya yi a kansu, cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi.

Tsohon gwamnan Legas kuma wanda ya ayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar shugaban ƙasar Najeriya ya faɗi hakan ne a ziyarar da ya kai wa Alaafin na Oyo Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadi.

Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama.

An ambato Tinubun na cewa: "Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari? Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa." Majiya: B B C

Post a Comment

0 Comments