Majalisar Wakilan Najeriya ta karɓi rahotanni 68 na ƙudirorin yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 kwaskwarima a yau Laraba.
Majalisar ta saka ranar 2 ga watan Maris a matsayin ranar da 'yan majalisar za su fara jefa ƙuri'a na tsawon kwana biyu kan batutuwan da gyaran zai shafa.
Mataimakin Kakakin Majalisa Ahmed Idris Wase ne ya gabatar da rahotannin wanda kuma shi ne shugaban kwamatin gyaran.
Tanadin Kundin Tsarin Mulki ya buƙaci cewa duk ƙudirin da ke son sauya wani ɓangare na kundin sai ya samu amincewar biyu cikin uku - 240 na wakilai 360 - kafin ya zama doka.
0 Comments