Kisan Hanifa: Kotu Ta Dage Sauraren Karar A Kano




BBC ta labarto cewa; kotun majistare da ke sauraren karar kisan da aka yi wa yarinyar nan 'yar shekara biyar a Kano, Hanifa Abubakar, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wadanda ake zargi da kisan har zuwa 9 ga watan nan na Fabrairu 2022.


Lauyoyin gwamnati karkashin jagorancin Barista Aisha Mahmud ne suka nemi a sake tsare mutane hudun da ake zargi har zauwa nan da mako guda da za su gurfanar da su a wata babbar kotu da ke da hurumin sauararen kara, kasancewar kotun majistaren ba da ta hurumi.

An kai babban wanda ake zargi da kisan, Abdulmalik Tanko wanda shi ne mai makarantar su marigayiyar, tare da sauran mutum uku gaban kotun majistaren a Gidan Murtala da ke birnin na Kano, yau Laraba.

A farko-farkon watan Janairu ne aka gano gawar Hanifa bayan sace ta da kuma hallaka ta ta hanyar ba ta maganin kashe bera a cikin shayi.

Batun kisan yarinyar ya tayar da hankalin jama'a tare da daukar hankali a Najeriya.

Daga bisani wasu matasa sun kona makarantar su yarinyar sakamakon tunzura su da lamarin ya yi.

Kungiyoyin kare fararen hula musamman kungiyar mata lauyoyi na daga cikin wadanda suka halarci zaman kotun na yau.

An kara yawan jami'an tsaro a harabar kotun.

Post a Comment

0 Comments