Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da gidan rediyon Vision FM mai cibiya a Abuja, daga gabatar da fitaccen shirin nan nasa mai suna ''Idon Mikiya.‘‘
A wata takarda mai dauke da umarnin dakatarwar wadda hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta kasar (NBC), ta aika wa gidan rediyon ta ce ta dauki matakin ne sakamakon shirin da aka gudanar na kai tsaye a tashar ranar 5 ga watan Janairu 2022 da kuma tashar talabijin ta Farin Wata.
Sanarwar ta ce a shirin ranar wanda aka tattauna batutuwa ciki har da na nadin mukamai a Hukumar Bayanan Sirri ta Kasa (National Intelligence Agency, NIA), tashar ta saba wa tsarin mulki na Nijeriya, sashe na 39(3)(b), wanda ya takaita magana a kan abubuwan da suka shafi hukumomin tsaro na gwamnati.
Hukumar ta ce a lokuta da dama ta gayyaci hukumar gidan rediyon na Vision FM a kan batutuwan da suka shafi aikin yada labarai, na tabbatar da adalci ga kowane bangare da ji daga kowane bangare da labari ya shafa da kuma kauce wa bayyana ra’ayin mai gabatar da shiri, wadanda dukkaninsu sun saba wa dokokin yada labarai.
A dangane da hakan ne hukumar ta dakatar da tashar daga watsa shirin tun daga ranar 28 ga watan Janairu 2022, tsawon wata shida, tare kuma da cin tarar hukumar rediyon naira miliyan biyar.
0 Comments