Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya zaɓi Sanata Muhammad Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakinsa, tare da miƙa shi gaban majalisar dokoki

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya zaɓi Sanata Muhammad Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakinsa, tare da miƙa shi gaban majalisar dokoki.

Hakan ya biyo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci da majalisar ta yi, jim kaɗan bayan tsige tsohon mataimakin gwamnan Mahdi Aliyu Gusau.

Sai dai a zaman shugaban majalisar, Nasiru Mua’zu ya karanta wasikar da gwamnan jihar Bello Matawalle wadda ya aike da sunan Sanata Muhammad a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa sabon mataimakin gwamnan Sanata Hassan yana wakiltar mazaɓar Zamfara ta tsakiya.

Post a Comment

0 Comments