Bayani dalla-dalla kan yadda Abba Kyari ya shiga hannun NDLEA

Bayani dalla-dalla kan yadda Abba Kyari ya shiga hannun NDLEA

Fassarar Dakta Furera Bagel

A ranar Juma'a 21 ga watan Janairu, 2022 ne,  da Æ™arfe 2 da minti 12 na rana, DCP Abba Kyari ya kira É—aya da ga cikin jami'an Hukumar YaÆ™i da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA a garin Abuja. 

Bayan minti biyu da kiran, sai shi jami'in ya mayar da kiran da ya yi masa. Sai Kyari ya ce masa zai zo wajensa bayan sallar Juma'a don su tattauna wata magana da ta shafi aiki.

Sai su ka haɗu a wajen da su ka shirya haduwar, kuma kai tsaye shi Abba Kyari ya fara bayani da cewa, yaransa sun kama wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi da su ka shigo ƙasar nan da ga Ethiopia ɗauke da hodar Ibilis mai nauyin Kilogiram 25.

Abinda yake so shi ne, shi da yaransa zasu É—auki kilo 15, su bar kilo 10 wanda da su ne za’a yi amfani wajen gurfanar da waÉ—annan masu safara a kotu a Enugu, inda a ka kama su.

Sannan kuma kilo 15 da Kyari da yaransa zasu É—auka, sai a maye gurbinsu da hodar boge ta daidai yawan kilo 15 É—in da ya É—auka, yanda ba za a gane ba.

Abin da ya ke so da wannan jami’in na NDLEA shi ne ya taimaka wajen shawo kan manyansa na ofishinsu da ke Abuja,  da su yarda da wannan shiri nasa.

Da Æ™arfe 11:05 na safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Janairu, bayan hukumar ta bashi izininin nuna wa Abba Kyari cewa sun yarda da shirinsa, sai jami’in da  Kyari É—in su ka ci gaba da yin wayar bidiyo ta WhatsApp a gaba É—aya wannan rana, inda ya faÉ—a masa cewa an yarda su ci gaba da wannan harÆ™alla.

Daga nan ne Abba Kyari ya faÉ—a masa cewa har sun raba kilo 15 É—in da ya É—auka shi da masu kawo bayanai (informants), waÉ—anda da su suka kawo masu labarin waÉ—annan masu safara. Inda su ka baiwa informants É—in kilo 7 shi kuma da yaransa sun É—auki kilo 8, har ma sun sayar da nasu kason.

Da ga nan ne sai ya ce ya na so shi ma wannan jami’in da mutanensa na hukumar, reshen Abuja su ci moriyar wannan harÆ™alla, inda ya ce in sun yarda zai sayar da 5kg daga cikin wancan kilo 10 da ya rage ya kawo masu kudin. Sai ya rage 5kg kawai na zallar hodar Ibilis da za a kai kotu sauran kuma a sa na boge.

Tun da a na sayar da kowane kilo na hodar ibilis É—in kan Naira Milliyan 7, to kuÉ—in da zai kawo masu akan wannan kilo 5 É—in zai zama naira miliyan 35, kenan. A dalar Amurka kuma ya kama $61,400 kenan.

Da ga nan ya matsa wa jami’in cewa ya kamata ofishin ma su na Abuja su karÉ“i su waÉ—anda a ke tuhuma da kuma sauran hodar Ibilis É—in da ga hannunsu tunda suna nan a Abuja. Shi kuma ya ce yana wayar ne daga Legas i

Post a Comment

0 Comments