Ba so muke Muna kashewa ana kashe mu ba, Munfi son Zaman lafiya.... -Con. Muhammad J. Abubakar 17 Birget Katsina, a wajen taron A.Y.D.F
A yau Lahadin 20 ga watan Fabrairu, Kungiyar AREWA YOUTH DEVELOPMENT FORUM, ta gudanar da Bikin Ƙaddamarwa da Rantsar da Shuwagabannin ta na jihar Katsina, tare da gabatar da ƙasidu masu taken: "Illar Kafafen sada Zumunta da yanda suke shafar karatun ɗalibai a makarantu" sai "Illar Bangar Siyasa (sara suka) ga rayuwar Matasa" kasidun waɗanda aka bawa hakkin su yanda ya kamata daga bakin zakakuran Matasa ɗalibai, wanda suka samu ta'aliƙi daga bakin Farfesa Muhammad Ahmad, Mataimakin VC na Jami'ar Ummaru Musa Yar'adua, da Malam Abubakar Abdullah Mashi. Dukkanin su sunyi kira sunyi nuni da jan hankali ga Matasan da jinjina garesu bisa irin kwazon su. A nasa jawabin Wakilin 'Yansanda na Area Commonder, ya ja hankali da kira ga ita wannan ƙungiya tas maida hankali wajen tallafawa Marayu wadanda suka rasa iyayensu, lura da basu tarbiyya da daukar ɗawainiyar wani bangare na Rayuwar su, yace "Mafi ya yawa daga cikin bata garin da ake fama dasu, sun girma da a gaban iyayen su ba babu tarbiyya babu ilimi dole a faɗa mummunar sana'a' inji shi.
Shima wakilin Shugaban Soji na 17 Birget dake katsina, Kanal Muhammad J. Abubakar yayi kira ga Matasan da su sanya hikima wajen nusarwa da wayar da kan al'uma musamman kan wannan Ta'addancin dake faruwa na sace mutane a wasu ƙauyuka, "Ba son mu bane muje daji muna kashewa ana kashe mu ba, munfi farinciki da zaman Lafiya, Mutane ne a cikin kauyuka, babu jami'an tsaro daga su sai 'yan ta'adda kusa dasu, sun hanasu Noma da duk wani nau'in Kasuwanci, dole su zama masu taimakawa ɓarayi domin su tsira daga Sharrin waɗannan ɓata garin." Inji Kanal. Ya ƙara kira da cewa ita wannan ƙungiya yana da kyau ta lura ta kuma jawo hankali a kan Illar alaka da ɓata gari.
Taron da aka gudanar a harabar Sakatariyar ƙaramar Hukumar Katsina ya samu halartar
Manyan baki da suka haÉ—a da: Shugaban Jami'ar Umaru 'Yar'adua, Farfesa Mahmud Ahmad, da dan majilisa mai wakiltar karamar hukumar jihar katsina a majalissar dokokin jiha, Honorabul Alhaji Ali Abu Albaba, da Wakilin Area Commander, da Wakilin Birgediyar Soji ta 17, (17 Birget) da Wakilin Sarkin Katsina, da Uwar kungiyar a matakin jiha, Hajiya Hadiza Yunusa Ingali, da kuma shugaban kungiyar na kasa baki daya, Kwamared Husaini Isma'il.
0 Comments