An rantsar da Sanata Hassan Muhammad Nasiha a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara.
Alƙaliyar Alƙalai ta Zamfara Kulu Aliyu ce ta rantsar da sanatan a yau Laraba bayan 'yan majalisar dokokin jihar sun tsige Mahdi Aliyu Gusau daga muƙamin.
A yau Laraba ne Kakakin Majalisar Dokoki Nasiru Muazu Magarya ya karanta wasiƙar da Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya aike musu ta neman tantancewa da naɗa Sanata Nasiha a matsayin mataimakinsa.
0 Comments